1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'yoyin jaridun Jamus

YAHAYA AHMEDNovember 18, 2005

A sharhohin da suka buga kan nahiyar Afirka a wannan makon, mafi yawan jaridun Jamus sun fi mai da hankalinsu ne kan zabukan da aka gudanar a kasashen Laberiya da kuma Burkina Faso. Sai kuma labarin kame tsohon shugaban kasar Cadi, Hissene Habre da aka yi a birnin Dakar na kasar Senegal, wanda shi ma ya sami shiga a jerin sharhohin jaridun na Jamus.

https://p.dw.com/p/BvQE
Ellen Johnson-Sirleaf
Ellen Johnson-SirleafHoto: AP

Da farko za mu waiwaya ne zuwa kasar Laberiya, inda al’umman kasar suka ka da kuri’u a zagaye na biyu, a makon da ya gabata, don zaban sabon shugaban kasarsu, bayan shekaru da dama da aka shafe ana ta gwabza yakin basasa a wannan kasa. Zaben dai yana muhimmanci kwarai ga gamayyar kasa da kasa, wadda ke ta kokarin ganin cewa, Laberiyan ta farfado daga yakin basasan ta kuma tsaya kann kafafunta. A cikin sharhin da ta buga game da zaben, jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi la’akari ne da cewa, a karo na farko a tarihin nahiyar ta Afirka, za a sami shugaban kasa mace, wadda kuma zabanta aka yi a wannan mukamin. A ganin jaridar dai, nasarar da Ellen Johnson-Sirleaf ta samu a zaben, ta dace da yadda aka ka da kuri’un da kuma sakamakon wucin gadin da aka bayyanar. Koke-koken da abokin hamayyarta, tauraon kwallon kafar nan George Weah ke yi, na cewa an tabka magudi a zaben ne, ba su da tushe. Saboda bayan an kirga kusan kashi 96 cikin dari na kuri’un da aka ka da, Johnson Sirleaf din ce ke kan gaba. Kazalika kuma, duk masu sa ido a zaben sun ce ya wakana ne cikin kwanciyar hankali da kuma adalci.

Duk da cewa, George Weah, mai shekaru 39 da haihuwa, ya fi Johnson-Sirleaf farin jini a kasarsa, amma, mafi yawan masu ka da kuri’un ba su ba da muhimmanci ga tashen da ya yi tamkar tauraron wasannin kwallon kafa ba. Ban da dai kwarewar da ya yi a wasannin kwalon kafar, George Weah, ko takardar shaidar gama karatu ba shi ita, kuma ba shi da wata cudanya da harkokin siyasa, inji jaridar. Watakila hakan ne ma ya sa ya sha kaye a zaben.

A daura da Weahn kuwa, Ellen Johnson-Sirleaf, mai shekaru 67 a duniya, ta shafe fiye da shekaru 30 tana gwargwarmaya a fannin siyasa. Ta dai yi karatu mai zurfu a jami’ar Havard a Amirka. Sa’annan kuma ta yi aiki a bankin duniya. Ta kuma rike mukamin shugaban reshen Afirka na Hukumar kula da shirye-shiryen raya kasashe ta Majalisar dinkin Duniya. Ta kuma jagoranci jam’iyyun adawa a kasarta a lokacin mulkin Samuel Doe da Charles Taylor. Sau biyu ma ana daure ta a kurkuku, saboda kalubalantar da take yi wa hukumomin wannan lokacin.

Jaridar dai tana yi wa Ellen Sirleaf Johnson ne fatan alheri, da kuma kira ga duk al’umman kasar gaba daya, da su hada kai wajen sake gina kasarsu, wadda yakin basasa na shekaru da dam ata ragargaza.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi buga wani rahoto ne kan kame tsohon shugaban kasar Cadi, Hissene Habre da aka yi a ran talatar da ta wuce a birnin Dakar, a can kasar Senegal. Dalilin cafke tsohon shugaban da aka yi kuwa, shi ne izinin kasa da kasa na neman a tsare shi da wata kotun kasar Belgium ta bayar a cikin watan Satumban da ya gabata, inda ta zarge shi da take hakkin dan Adam, da azabtad da masu adawa da shi da aka tsare, da kuma kisan da aka yi wa da yawa daga cikinsu, a lokacin mulkinsa. Tun hambarad da shi da aka yi a cikin shekarar 1990 ne yake zaman gudun hijira a kasar Senegal.

Wasu `yan kasar Cadin, wadanda suka sha azaba a hannunsa, wadanda kuma yanzu ke da takardun kasar Belgium din ne suka kai kararsa gaban kotu a birnin Brussels, tare da daurin gindin da suka samu daga kungiyar nan ta Human Rights Watch.

Jaridar die Tageszeitung kuma, ta yi sharhi ne kan zaben kasar Burkina Faso, inda ta ce, a nahiyar Afirka dai, ko wane shugaba zai iya dawwama kan mulki ne har zuwa tsawon duk lokacin da ya ga dama. Duk da cewa, tafarkin dimukradiyya ba ta amince da yin hakan ba, amma salon da wasu shugabannin nahiyar dai ke bi ke nan. A lal misali kamar a Burkina Faso. Da farko dai, shugaban kasar, Blaise Compaore, ya fara hawar karagar mulki ne, ta juyin mulkin soji, inda ya shafe shekaru 4 yana mulki. Bayan haka ne, ya jagoranci tsara kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya ba shi damar ci gaba da shugabancin, a wa’adi biyu, ko wanne mai tsawon shekaru 7. To bayan wadannan shekaru 14 ne kuma, ya kirkiro wani salo, inda aka yi wa kundin tsarin mulkin garambawul, na bai shugaban kasar da za a zaba wa’adi biyu ko wanne mai tsawon shekaru 5. Amma tun da wannan sauyin da aka yi wa kundin, ba ya la’akari da shekaru baya, wato shugaba Compaore, zai iya ci gaba da mulki ke nan har tsawon wasu shekaru 10 ma masu zuwa nan gaba. Idan dai aka lissafa, wato zai iya kasancewa kan karagar mulkin kasar ke nan har zuwa shekara ta 2015.

Zaben da aka gudanar a kasar dai na nuna cewa, shugaba Compaoren ne ya ci nasara, da samun kashi 70 cikin dari na kuri’un da aka ka da. To ko ina aka nufa da tafarkin dimukradiyya a nahiyar Afirka ?