1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

081010 Adoption Afrika

October 14, 2010

Matukar babu kyakyawar kulawa, to lallai yaro bai zai samu goyon bayan da ake bukata ba.

https://p.dw.com/p/PcjQ
Rayuwar kananan yara.Hoto: Steffen Leidel

Rayuwar ya' ya'yen da iyayen su ke cikin halin talauci a nahiyar Afirka na cikn wani hali, inda yaran ke tsintar kawunan su cikin wasu sabbin al'adu ba kuma tare da fuskantar harshe ko sanin makomar sake haduwa da iyayen su a nan gaba ba. Irin wadannan iyaye dai sun zabi bayar da ya yansu ne ga mutanen dake neman mayar da ya' yan wasu nasu, musamman ma a nahiyar turai. Lamarin da a yanzu ya zama wata dama ga masu neman ya ya, kana hanyar samun sauki ga iyaye matalauta.

A kwai hotona like a wurare daban daban na shahararriyar mawakiyar nan yar asalin kasar Amurka Madonna tare da wani karamin yaro. Mayar da dan wani nata da ta yi, na cigaba da jawo hankalin al'umomin kasa da kasa dama masu suka, lokacin da aka samu labarin cewa yaron ba maraya ba ne. To amma Madonna, ta hakikance cewa tana bawa yaron kyakyawar kulawar da zata amfane shi a gaba. Irin wannan tunani ne dai iyaye da dama a kasashen yamma keda shi. A cewar kungiyar kare hakkin kananan yara ta (save the children) diyan ta ya yan wasu da mutane ke yi na karuwa sosai da sosai tsakanin maaurata a kasashen yamma, inda sukan garzaya zuwa nahiyoyin Afirka da Asia da nufin samun yara. Misali a nahiyar Afirka, kasar Ethiopia keda mafi yawan yaran da turawa suka mayar da su ya' ya', musamman ma a kasashen Amurka, Austaralia da sauran su.

Susanne Christensen, ita ce shugabar kungiyar (save the children) ta kasar Denmark a Ethiopia, ta kuma bayyana irin yadda take ganin iyaye na azama wajen bayar da ya yansu.

" Basu san doka ba, kana basu san halin da ya yan su ke shiga ba. Abinda ke gaban su shi ne, su samu dan abinda zasu sa a aljihun su, inda suke tunanin hakan zai kyautata yanayin rayuwar su"

A cikin kasar da gwamnati bata tallafawa iyalai mabukata, ko kuma samarwa da kungiyoyin kula da marayu da marasa galihu wani taimako, bayar da yara ga masu nema abu ne mai sauki. A dokar kasar ta Ethiopia, ba a yarda a bayar da yaro ba matukar daya daga cikin iyayen sa na da rai. To amma duk da haka ba a samu raguwar irin wannan dabi'a ba a cewar Christensen.

" Akwai kungiyoyi da dama dake nazartar iyayen dake son wasu su mai da ya yansu nasu, mutanen basu gane ba ne, domin ana ce musu nan bada jimawa ba za a dawo musu dasu. Bugu da kari kuma, ga kudi mai tsoka a wannan harka, lamarin da ka iya haifar da cin hanci, wannan abu ne mai matukar sarkakiya"

Kinder vor einem Fahrzeug des Malteser Hilfsdienstes
Hoto: picture-alliance/ dpa

A daya bangaren kuma, kasar Ghana ita ce aka fi samun karancin mayar da ya'ya hannun sabbin iyaye, duk kuwa da cewa karkashin dokar kasar ana iya diyauta ko wane yaro ba sai maraya ba. Reverend Emmanuel Kwasi Nkuruma, darakta ne a asusun biyan diyya ga al'umma a kasar ta Ghana, ya kuma ce shi bai ga wani abin kaico ba kan diyauta yaran da turawa ke yi.

" A gani na diyauta da a ciki ko wajen Ghana wani abin maraba ne, saboda yaro zai shiga cikin wata sabuwar al'ada, wadda a cikin ta ilimi yake da muhimmanci kana kuma ya samu kyakyawar kulawa"

Lallai akwai kulawa. to amma ta saba da dokokin da aka amince da su a taron MDD kan yancin kananan yara, wanda aka ayyana diyauta dan wani a matsayin mataki na karshe. To amma har wa yau Reverend Nkurumah, yace wannan abu na samarwa da yaro cigaba ne, maimakon kudin da ake kallon suna fadawa hannun wasu miyagun mutane ba.

" Matukar babu kyakyawar kulawa, to lallai yaro bai samu goyon bayan da ake bukata ba. Haka ne yasa a wasu lokutan ake samun matsala kan yara a kasashen su"

Can a sauran kasashen duniya kuwa, dokokin diyauta yara na da matukar tsauri, inda yake zama abu mai dan karan wuya yaro ya bar kasar sa ta haihuwa. Misali a kasar Uganda, doka ta bukaci duk mai son mai da dan wani nasa ya zauna a kasar har na tsawon shekaru 3, kana kuma ya rike yaron na kwatankwacin haka. Inda a kasar Nepal kuma ake kallon wannan harka a matsayin ta tsofaffi, kana kuma gwamnati ke da hannu wajen gudanar da ita.

Mawallafa : Jane Ayeko /Tukur Garba Arab

Edita : Abdullahi Tanko Bala