1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rice a Beijing

Zainab A MohammadOctober 20, 2006
https://p.dw.com/p/Btxf
Rice da Shugaba HU na Sin
Rice da Shugaba HU na SinHoto: AP

Acigaba da rangadin neman goyon bayan wa Amurka dangane da kasar koria ta Arewa a yankin Asia,ayau ne sakatariyar harkokin wajen Amurkan ,Condoleeza Rice ta isa birnin Beijing din kasar.

Da saukar ta Beijin dai,Jamiin kasar ta Sin ya fadawa Condoleeza Rice cewa,ganawarsa da shugaba Kim Jong Il na koriya ta arewa,bisa dukkan alamu zai haifar da da mai idanu,akokarin da kasar takeyi wajen jan hankalin koriyan komowa teburin tattaunawa da kuma dakatar da shirin nuclearnta.

Jakadan Sin zuwa koriya ta Arewan Tang Jiaxuan,ya fadawa sakatarin harkokin wajen Amurkan cewa,duk da jan hankalin gwamnatin Pyonyang da yayi a ziyarar daya kai kasar a jiya,shugaba Kim bai nuna alamun zai bada kai bore ya hau dangane da kiraye kirayen kasashen duniya ba.

Shi kuwa Premiern Sin Wen Jiabao,cewa yayi a yanzu haka an cimma wata madafa a bangarorin biyu,adangane da kira da akewa koriya ta arewa ta komo teburin tattaunawa,domin kawo karshen shirin Nuclearnta.

Ya fadawa jakadar Amurkan cewa,ayanzu haka dai ana kokarin ganin cewa an warware wannan takaddama ta koriyabn,domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyan hankali a yankin arewacin Asia dama duniya baki daya.

Mr Wen yace babu wata hanya data wuce ta diplomasiyya da tattaunawa,domin gano bakin zaren warware wannan rikici.

Tun da farko dai Condoleeza Rice da ministan harkokin wajen Sin Li Zhaoxing sunyi kira ga koriya ta arewan data koma tattaunawar kasashen shida akan harkokin nucleanta,ba tare da gindaya sharudda ba.

Sakatariyar Amurkan tace Bangasrorin biyu sun jaddada manufofinsu na sake farfado da wannan tattaunawar ,wadda ta hadar da Amurka da koriya ta arewan data kudu,da ita kann ta Sin da Japan da Rasha.

"Rice tace mun jaddada barin kofa bude dangane da tattaunawar kasashen shida,saboda shugaba Bush da takwaransa Sin Hu,sun lashi takobin daukan matakan diplomasiyya wajen warware matsalart,wanda zai fara da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen shida a watan satumban shekarata ta 2005."

Kazalika ta fadawa manema labaru cewa sun tattauna batun aiwatar da kudurin mdd na dubu 1 da dari 7 da goma sha 8,wadda ke bada damar kakabawa koriya ta arewa takunkumi,sakamakon gwajin makaminta da ta sanar da yi a ranar 9 ga watan oktoba.

Anashi bangaren ministan harkokin wajen Sin Mr Li yace kasar Sin zata cigaba da sauke hakkin daya rataya a wuyanta,tare da darajawa dokar kasa da kasa.

Bugu da kari yace Sin zatayi amfani da hanyoyi na diplomasiyya wajen tabbatar dacewa koriya ta amince da komawa teburin tattaunawa nan na kasashe shida,akan harkokin nuckleanta.