1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rice a yankin gabas ta tsakiya

October 15, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8S

Sakariyar harkokin wajen Amurka ta saurarai bayanan shugaba Mahmud Abbas na yankin Palasdinawa dangane irin rawar da yake bukatar Amurka ta taka ,a taron sasanta yankin da zata dauki nauyin gudanarwa,wanda kuma ya sha banban dana bangaren Izraela.Yankin palasdinawan dai na bukatar a tsara wani daftari na hadin gwiwa,da Izraels,wanda zai bayyaana yadda zaa shawo kann manyan matsalolin dake haifar da rikici.Kuma dole ne a kammala rubuta wannan Daftari kafin a fara gudanar da wannan taro,domin ayi amfani dashi a matsaayin tubalin fara tattaunawar sulhunta bangarorin biyu,inji Palasdinu.A yayinda a bangarenta Izraela tace zaa iya gudanar da wannan taron ba tare an gabatar da wannan takarda ba,tare da watsi da batun kayyade lokaci na fara tattaunawar szulhunta bangarorin biyu.Sai dai majiya daga aMurkan na nuni dacewa zaa iya dage taron wadda aka tsayar da fara shi a karshen watan nNuwamba,saboda wannan sabani dake tsakanin bangarorin biyu.