1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rice ta kammala balaguro a Gabas Ta Tsakiya

July 25, 2006
https://p.dw.com/p/BupA

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta kammala wani rangadi na diplomasiya a yankin GTT wanda ya mayar da hankali akan fadan da ake yi tsakanin Isra´ila da ´yan yakin sunkurun Hisbollah. Bayan tattaunawar da ta yi da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a birnin Ramallah, Dr. Rice ta ce da akwai bukatar a ci-gaba da mayar da hankali wajen kafa kasar Falasdinu mai makwabtaka da Isra´ila, duk da rikicin da ake fama da shi a Libanon. Rice ta ce al´umar Falasdinawa sun kasance cikin tashe tashen hankula na lokaci mai tsawon gaske.