1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Richard Clarke da George Tenet sun bayyana a gaban kwamitin binciken hare-haren 11 ga watan saatumba.

Mohammad Nasiru AwalMarch 25, 2004
https://p.dw.com/p/Bvl5

Richard Clarke dai ya shafe shekaru da dama yana matsayin daya daga cikin manyan jami´ai dake bawa gwamnati shawara game da ayyukan ta´addanci a karkashin shugaba George Bush Senior da shugaba Bill Clinton da kuma shugaba mai ci GWB, kafin ya yi murabus. Shi ne kuma ya kirkiro wani tsarin kare sararin samaniyar Amirka daga hare-hare na ta´addanci a lokacin wasannin olympics da aka yi a birnin Atlanta a shekarar 1996 sannan kwanaki kalilan gabanin harin ran 11 ga watan satumba, ya fid da wani littafi mai bayani game da mummunan tasirin da wani harin ta´addanci zai yiwa Amirka.

Yanzu dai yana zargin shugaba Bush da yin watsi da gargadin da aka yi ta masa game da barazanar da ake fuskanta daga kungiyar Al-Qaida tun gabanin ran 11 ga watan satumban shekara ta 2001. Clarke ya ce a cikin watanni 8 na farko bayan da Bush ya haye kan karagar mulki, gwamnatinsa ba ta dauki matsalar ta ta´addanci da muhimmanci ba, sannan ya kara da cewa:

"Mamaye kasar Iraqi da shugaban Amirka ya yi, ya janyo babban koma baya ga yakin da ake yi da ´yan ta´adda."

A cikin wadanda suka ba da shaida a gaban kwamitin binciken Clarke ne kadai ya nemi gafara daga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren na 11 ga watan satumba, saboda gazawar gwamnati, sannan ya ce:

"Gwamantin ku, wadda zata kare ku ta kai ku ta baro. Lalle na gaza."

Da farko daraktan hukumar leken asirin Amirka CIA, George Tenet ya amsa cewar hukumarsa ta gaza dangane da hare-haren.

Tenet wanda ke jagorantan hukumar ta CIA tun a shekarar 1997, ya ce tun a cikin shekarar 1996 lokacin gwamnatin shugaba Bill Clinton hukumomin Amirka ke bin diddigin ayyukan shugaban kungiyar Al-Qaida Osama Bin Laden. Sannan a lokacin bazara na shekara ta 2001 an samu bayanai game da harin ta´addanci to amma an yi zaton kai wannan hari a ketare ne. Tenet ya ce yanzu haka kungiyar Al-Qaida na shirin kai wasu hare-haren a cikin Amirka. Shi kuwa a nasa bangaren mai bawa tsohon shugaba Bill Clinton shawara game da harkokin tsaro Sandy Berger cewa yayi tun bayan hare-haren da aka kaiwa ofisohshin jakadancin Amirka a Tanzania da Kenya a shekarar 1998, ya fito fili cewar Amirka na cikin wani yaki da kungiyar Al-Qaida. To amma mamaye kasar Afghanistan inda Al-Qaida ke da sansanonin horas da mayakanta a shekara ta 2001, bai cimma manufar da aka sa a gaba ba.