1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigimar 'yan siyasar jihar Rivers ta munana

Mohammed Bello/MNAMarch 9, 2016

Tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa a jihar ta Rivers, sun fara kashe guiwar masu son yin aikin zabe na 'yan majalisar kasa da na jiha.

https://p.dw.com/p/1IA5N
Wahl in Nigeria
Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde

Tun dai bayan rigingimu da tashe-tashen hankula da suka hada da kashe- kashe tare da salwantar dukiyoyi da aka yi ta yi a jihar Rivers gabanin zaben shekara ta 2015 da kuma bisanin zaben, tashe-tashen hankulan dai za a iya cewa sun sake dawowa, musamman ba dadewa da kotun koli ta tabbatar da zaben Gwamna Nyesom Wike na jam'iyyar PDP a jihar.

Ko da yake wasu tashe-tashen hankula ana danganta su da adawar 'yan kungiyoyin asiri a jihar, sai dai masu la'akari da siyasa cikin wannan tashin hankali sun fi yawa.

Gwamnan jihar dai Barister Nyesom Wike ya musanta cewar kashe-kashen da ke faruwa ba 'yan siyasa ciki face fa 'yan kungiyoyin asiri ne.

Akwai dai sake zabe na sanatoci da 'yan majalisun tarayya da na jiha a Rivers din, nan da 'yan kwanaki kadan, kuma batun wannan zabe an tabbatar shi ne ke dada assasa gararin da ke kasa a yanzu.

Rigingimun dai sun zama ruwan dare

Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Hoto: picture-alliance/dpa/Tife Owolabi

Bayan dai kashe-kashe a shiyyar Ogoni da garin Omoku da aka kille wa wani kai tare da kashe iyalansa kaf, sai kuma a baya bayannan a garin Buguma, inda bayan lallasa wani dan siyasa aka zazzaga masa fetur tare da cinna masa wuta, kuma da haka yace ga garinku nan.

Wata ce da ta shaida tashin hankalin yankin Ogoni a baya bayan nan, inda bayan kashe-kashe, an kuma banka wa ofishin Sanata na shiyyar wuta cewa ta yi:

"Musayar wuta ce kawai ake yi tsakanin kungiyoyin asiri, kuma kowa na ta kansa, don karar tashin bindigogi ne kawai kake ji."

Rundunar 'yan sandan jiha dai ta jagoranci gudanar da tarurruka a baya bayan nan kan wannan tashin-tashina da ta ki ci ta ki cinyewa, inda kwamishinan 'yan sanda Musa Kimo ke fadi a taron.

"Bari in jaddada batun tsaro, domin in ba tsaro, ba dayan mu da zai kasance a nan, muna kuma magana ne kan rayukan jama'a da kuma dukiyoyinsu, kuma abinda muka damu da shi ke nan. Don haka wajibi ne na dada bayyana ayyukanmu na tsaro gareku."

Ga dukkanin alamun abinda ke faruwa yanzu, wannan taro na jami'an tsaro da daukacin masu ruwa da tsaki kan tsaron jihar, musamman ma 'yan siyasa, bai kai ga tasirin da ake fata ba.

Janyewa daga aikin zabe saboda fargaba

Wahl in Nigeria
Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde

Tuni ma dai wasu malaman jami'ar Fatakwal da za su yi aikin jami'an zaben da za a sake gudanarwa na 'yan majalisu din, suka bayyana janyewarsu daga shiga aikin, sannan akwai wasu Jam'iyyun ma da suke tunanin janyewa sakamakon hangen gararin da ke kasa, musamman ma bisa furucin Gwamnan jihar cewar, duk wani ko wasu da ke shirin yin magudin wannan zabe, to ya fara rubuta takardar wasiyya tukuna, furucin kuma da Gwamnan yai ta nanatawa a kafofin rediyoyi na jihar.

Wasu kungiyoyi na ciki da kuma na kasa da kasa a jihar ta Rivers, sun yi kira da a kawo karshen rigimar ta 'yan siyasar jihar. Kungiyoyin su kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da ke afkuwa a jihar.