1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riikicin Kurdawan arewacin Iraki da Turkiyya

October 25, 2007
https://p.dw.com/p/C15i

Shugaba Abdullah Gul yayi gargadin cewar ,hakurin turkiyya na neman karewa adangane da yan adawan kurdawa dake arewacin Iraki,bayan da dakarun gwamnati suka sanar da mayar da martani kann harin da mayakan kurdawan suka kai musu.A yanzu haka dai Ankara ta jibge dakarunta kimanin dubu 100,a tsaunuka dake kann iyakakokin kasashen biyu,wanda ke nufin kowane lokaci daga yanzu zasu iya kutsawa,domin murkushe yan jamiyyar kurdawa ta PKK ,wanda yawansu bai shige 3,000.Jamian Diplomasiyyan Iraki da Amurka da Turkiyyan dai,sun dauki matakai na kare babban kutse da da dakarun turkiyyan zasu iyayi.Sai dai Turkiyyaa dake zama wakiliyar kungiyar tsaro ta NATo,tace bazata sake amincewa da hari daga kurdawan na PKK ba.