1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikice rikice na ci gaba da ruruwa a Somalia

December 25, 2006
https://p.dw.com/p/BuWY

Kungiyyar tarayyar turai tayi Allah wadai da tashe tashen hankula dake ci gaba da faruwa a kasar Somalia, tare da bukatar daukar matakan gaggawa na kawo karshen wannan al´amari.

Babban abin da yafi damun kungiyyar ta Eu a cewar, Jami´in ta mai kula da harkokin agaji da raya kasa, wato Louis Micheal shine na yadda aka samu hannun kasar Habasha a rura wutar wannan rikici.

Tuni dai faraministan kasar ta Habasha, wato Meles Zenawi yace kasar sa na yakin tsagerun kasar ta Somalia ne, a wani mataki na dasa danbar hana wannan rikici shigowa izuwa cikin kasar su.

Ya zuwa yanzu dai masana a harkokin soji sun kiyasta cewa akwai sojin kasar Habasha a kalla dubu 15 zuwa 20 a cikin kasar ta Somalia. Itama dai kasar Eritrea na da soji kusan dubu biyu, wadanda ke agazawa wadannan tsageru na Somalia.