1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikice-rikicen Iraki

Zainab A MohammadMay 31, 2005

Iraki da kewaye ayau Talata

https://p.dw.com/p/Bvba
Hoto: AP

Yau madai kamar yadda aka saba an wayi gari a kasar Iraki cikin cigaban tashe tashen hankula a sassa daban daban.Dakarun Amurka 4 dana Italiya 4 da wani dan kasar Iraki guda ne suka rasa rayukansu a hadarin jiragen sama,sai dai ya zuwa yanzu babu tabbacin kakkabo wadannan jiragen akayi ko kuma hadari ne kawai.

A birnin bagadaza kuwa Prime minister Ibrahim Jaafari yayi Allah wadan kamun shugaban jammiyar yan darikar sunni da dakarun Amurka sukayi a jiya,inda yace ya bukaci bayanai daga babban general na Iraki dangane da tsare Abdul hamid na tsawon saoi 12,wanda dakarun Amurkan sukace bias kuskure ne.

Kamun shugaban jammiyar darikar Sunni Mohsen Abdul-Hamid da Asubahin jiya dai ya dada watsar da dangantakar dake tsakanin alummomin darikar sunni da shia dake Irakin,abunda wasu suka bayyana zai iya jagorantar yakin batsatsa.

Shi kuwa shugaban Al qaeda a Iraki kuma haifaffen kasar Jordan Abu musab al-Zarqawi ,ya aikewa babban jagoran kungiyar Osama bin laden sako ta yanar gizo gizo cewa,inda yake tabbatar masa dacewa raunin daya samu ba mai hatsari bane,tare da watsi da rahotan dake nuni dacewa ya samu mummunan rauni.

A jiya nedai wani jirgin saman dakarun sojin Iraki ya fado a yankin arewa maso gabashin bagadaza inda ya kasha sojin Amurka hudu,da matukin jirgin wanda ke zama dan Iraki.Ayayinda cikin daren jiya kuma jirgin dakarun Italiya mai kirar saukan ungulu yayi hadari a garin Nassiriya dake kudancin kasar akan hanyarsa daga kasar Kuwaiti,matuka jirgin biyu da jamiai biyu dake cikinsa suka mutu nan take.Har yanzu dai babu tabbaci dangane da sanadiyyar wadannan faduwan jiragen biyu.

A makon nan kadai dai jiragen saman soji guda uku kenan suka yi hatsari,a ranar 26 ga wannan wata ne kuma dai yan yakin sari ka noken kasar suka kakkabo wani sojin Amurka,ayayinda yake wucewa ta sararin samaniyan garin Baquba dake arewaci.

A taron manema labaru daya gudanar a yau Premier Ibrahim Jaafari yayi alkawarin gudanar da bincike dangane da tsare jagoran jammiiyar yan darikar sunni da dakarun Amurka suka gudanar a jiya da yayansa uku.

A gaban majalisar dokokin kasar kuwa Jaafari yayi fatan cewa zaa gaggauta kamala tsara kundun tsarin mulkin kasar a tsakiyar watan Augusta.Bugu da kari yayi bayanin cewa tabbatar da tsaro a Iraki babban alhaki ne daya rataya a wuyan gwamnatinsa kuma abu mawuyaci.

A ranar lahadi nedai aka kaddamar da wani shiri na tabbatar da haske ta fanning tsaro wanda ya kunshi kimanin dakarun kasar dubu 40.Jaafari yace wannan shirin wanda ya kunshi bincike a dukkan sassan kasar ya fara haifar dad a mai idanu,domin anyi kame nay an Irakin da wasu na kasashen waje da ake zargi da aikata ayyukan tarzoma a cikin kasar.

Matsala guda dai injishi da ayanzu Irakin ke kokawa da shawo kansa shine tayar da boma bomai acikin motoci,inda a wannan wata kadai motoci 140 aka loda tare da tayar da boma bomai acikinsu,wanda ya kasha akalla mutane 750 da dakarun Amurka 70.

Ko ayau ma boma bomai sun tarwatse a wata babbar mota a kusa da wurin binciken sojoji a garin Baquba,harin daya kasha soji biyu nan take tare da raunana wasu tara.

Ayayinda a gunduwar Anbar dake yammacin Iraki kuma ke fuskatar tashe tashen hankula,an tsinci gawar Gwamna Raja Nawaf,mutumin da aka sace tun a farkon wannan watan,tare dana wadanda suka sace shi,bayan arangama da sukayi da dakarun Amurka,inji kakakin gwamnatin Irakin.