1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a fagen siyasar ƙasar France

Yahouza SadissouMay 17, 2006

Praministan ƙasar France Dominique de Villepin ya ƙetara rijiya da baya, a sakamakon yunƙurin tsige shi daga muƙami a majalisar dokoki

https://p.dw.com/p/Bu02
Hoto: AP

Praministan ƙasar France Dominique de Villepin ya ƙetara rijiya da baya, bayan da yan majalisar dokoki ,su ka kaɗa ƙuri´a, yammacin jiya, da nufin stige shi daga karagar mulki.

Yan majalisar dokokin Jam´iyar adawa ta PS ne, su ka ajje takardar mai buƙatar stige Dominique de Villepin daga muƙamin sa na Praminsita.

Shugaban jam´iyar adawa Fransois Holland, na zargin gwamnatin De Villepin da kasancewa yar dagaji, sannan ba ta tabuka komai, illa faɗace- faɗace, tsakanin ɓangarori masu daba da juna a jam´iyar UMP, dake riƙe da ragamar mulki.

Wannan jam´iya na fuskantar wani rikicin cikin gida tsakanin magoya bayan Praminista Dominique de Villepin, da na ministan cikin gida, Nicolas Sarkozy bugu da kari shugabanjam´iyar ta UMP, da a ke bayanawa a matsayin ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasar France, a shekara mai zuwa.

A baya bayan nan, rikici ya ƙara ƙamari tsakanin ɓangarorin 2, a sakamakon wata baddaƙala mai ɗauke da sunan Clearstream.

A wanan haraka mai hazzo a cikin ta,Nicolas Sarkozy na zargin Praminista da shafa masa, kashin kaji, tare da tuhumar sa,da mallakar wasu maƙudan kuɗaɗe a bankunan ƙetare.

A wani abun da ba a saba gani ba,a fagen siyasar ƙasar France, jam´iyar Francois Bayru mai sassaucin ra´ayi, wadda kuma ke da ƙawance da UMP, a majalisar dokoki, ta yi kira ga yan majalisar ta, su ka kaƙa kuri´ar amincewa, da kiffar da Praminsita Dominique De Villepin.

Saidai duk da tsaka mai wuyar da Praminisran ya shiga a halin yanzu, yan majalisar adawa, da ƙwarorin masu basu haɗin kai ,daga ɓangaran jam´iyu masu ragamar mulki ,basu cimma nasara ba.

A baki ɗaya, yan majalisa 190 su ka kaɗa ƙuri´ar amincewa da hamɓara da, gwammnatin De Villepin, daga jimmilar yan majalisa 577.

A sahiyar yau, larana shugaban ƙasar France, yayi kira da babbar murya, ga gwamnati, da ta maida hankali a kan ayyukan gabata, domin sake samun tabaraki daga al´ummar Kasar France.

A majalisar dokokin kuwa, nana gaba a yau ne, za a kaɗa ƙuri´a, a kan saban tsarin da ministan cikin gida Nicholas Sarkozy ya gabatar, a game da dokoki karɓar baƙi a France.

Ministan, zai fara rangadi ranar yau, a ƙasashen Mali da Benin, inda zai tantana da hukumomin ƙasashen a dangane da batun gudun hijira, da baƙin haure.

Wannan ƙasashe, na daga sashun ƙasashen Afrika da al´ummomin su ka yi kaka gida, a ƙasar France.

Albarakacin wani gagaramin buki, da ya haɗa shugabanin ƙasashen Afrika 8 jiya, a France, shugaban ƙasar Senegal Abdulaye Wade, ya bayyana rashin amincewa, da saban tsarin da ministan cikin gida, ya gabatarwa Majalisar Dokokin .