1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a nahiyar Afirka.

January 5, 2006

Tsohuwar karamar minista a ma'aikatar ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayyar Jamus, Ushi Eid, ta yi bayanai kan rikice-rikicen da suka ki ci suka ki cinyewa a nahiyar Afirka, a cikin wata fira da ta yi da gidan rtediyon Deutsche Welle.

https://p.dw.com/p/Bu2f
`Yan makaranta a nahiyar Afirka
`Yan makaranta a nahiyar AfirkaHoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

Ushi Eid, ba bakuwa ba ce a kan batutuwan da suka shafi rikice-rikice a nahiyar Afirka, saboda, a loakcin da take rike da mukamin karamar minista a ma’aikatar ma’ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayyar Jamus, ta sha kai ziyara a yankunan nahiyar da ke ta fama da tashe-tashen hankulla, kamar yankin Darfur da Laberiya da Ruwanda da dai sauransu. A halin yanzu dai, al’amura a wadannan yankunan sai kara tabarbarewa suke yi duk da yunkurin shiga tsakani da gamayyar kasa da kasa ke yi. To ko me yasa kafofi kamar Kungiyar Tarayyar Afirka, ko kuma Kungiyar Hadin Kan Turai, suka nuna alamun gazawa wajen tabbatad da zaman lafiya mai dorewa a nahhiyar ta bakar fata ?

A ganin Ushi Eid:-

„Ba a daukar matslolin ne da muhimmanci. Rikice-rikicen sun fi yadda ake zato ko kuma yadda muke karanta labaransu a jaridu tsamari. A lal misali mutanen yankin Darfur na bukatar zaman lafiya, kafin su iya sakewa su kama harkokinsu na halin rayuwa ta yau da kullum; kamar dai yadda aka cim ma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin yankunan kudancin Sudan da kuma gwamnatin tsakiya ta kasar. Akwai dai mai a kasar. Sa’annan kuma, akwai kasashen ketare da yawa da ke son kare maslaharsu. Ta hakan ne kuwa ake ta samun cikas a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wajen sanya wa Sudan din takunkumi game da batun yankin Darfur. A lal misali Sin, wadda ke da kujerar dindindin, da kuma Pakistan, wadda a halin yanzu ke da wakilci a kwamitin, dukkansu na da sha’awar samun mai daga kasar. sabili da haka ne suke adawa da duk wani mataki na sanya takunkumi.

Amma rikicin da kansa, ba rikici ne kan albarkatun man fetur ba. Rikici ne da ake yi kan tushen samun ruwa. Yana kuma da dalilai da yawa da ke janyo shi. Sabili da haka ne dai ba za a iya warware shi nan take haka nan ba. Bugu da kari kuma, yankin Darfur, yanki ne mai girman gaske, wanda girmansa ya kai na Faransa alal misali. To samad da zaman lafiya a wannan yankin kawai, da kuma sa ido kan kiyaye ka’idojin tsagaita bude wuta, aiki ne mai wuyar gaske. Abin farin ciki ne dai, gani yadda kungiyar Hadin Kan Turai ke tallafa wa kungiyar Tarayyar Afirka da kudade don cim ma wannan burin. A nan ma Jamus ta cancaci yabo, inda dab da kirismeti ne, majalisar dokoki ta Bundestag, ta tsawaita lokacin gudummowar jiragen saman da ta bayar don jigilar dakarun kare zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirkan zuwa watanni 6 nan gaba. Na yi imanin cewa, duk bangarorin na iyakacin kokarinsu. Sai dai wannan rikicin, rikici ne mawuyaci. Kuma za a dau lokaci kafin a iya tabbatad da cikakken zaman lafiya.“

Daya yankin da al’amura ke barazanar tabarbarewa kuma, shi ne yankin nan na iyaka, tsakanin Habasha da Eritrea. kasashen biyu dai sun taba gwabzawa da juna a wani mummunan yakin da suka yi a cikin shekara ta 2000. Yanzu kuma, an ata samun hauhawar tsamari tsakaninsu, a kan dai wannan yankin. Ko yaya Ushi Eid za ta kiyasci irin halin da ake ciki yanzu, a kan iyakar Habashan da Eritrea ?

„Babu shakka, wannan rikicin dai, rikice ne da aka manta da shi magaba daya. Kin ga dai har ila yau, ana tattauna batun Darfur a tarukan gamayyar kasa da kasa. To kamata kuwa ya yi a takalo wannan batun ma na Eritrea, saboda al’amura za su iya gocewa, su tabarbare, su gagariduk wani yunkuri da ake yi na sulhu, har su kai ga barkewar wani sabon yakì kuma. Kotun duniya dai, ta tabbatar da iyaka tsakanin kasashen biyu, wadda aka zayyana, kuma dukkansu suka amince da ita da farko. To daga baya ne kuma, Habasha ta canza sheka. A halin yanzu dai, Eritea na zargin Habashan ne da shirya afka mata da yaki. Sabili da haka ne kuwa, ita ma ta girke dakarunta a yankunan iyakar.

Fatarmu dai ita ce, kungiyar Tarayyar Afirka da kungiyar Hadin, su iya cim ma nasarar shawo kan Habasha, ta amince da iyakar da gamayyar kasa da kasa ta yarje a kanta.“