1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici Game Da Hukuncin Kotun Turai

September 2, 2004

Kafofin yada labaran Jamus sun bayyana bacin ransu a game da hukuncin kotun Turai dake birnin Strassburg dangane da abin da suke ganin tamkar wani yunkuri ne na kayyade 'yancin 'yan jarida a nahiyar Turai

https://p.dw.com/p/Bvgn

Ko shakka babu a game da cewar mutane masu tarin yawa na sha’awar samun rahotanni a game da gimbiya Caroline. Amma ba lalle ba ne ba a hada rahotannin da hotunanta lokacin da take cefane a kanti ko akan doki tana kilisa. Alkalan a kotun Turai dake birnin Strassburg sun yanke hukuncinsu ne bisa dalilin cewar an gabatar da hotunan a cikin jaridu da mujallu ne ba tare da an nemi izini daga ita gimbiya Caroline ta Monaco ba, alhali wannan lamari ne da ya shafi harkokin rayuwarta ta yau da kullum. Wato dai hukuncin na mai yin nuni ne da cewar tilas a rika yin sara tare da duban bakin gatari, ba tare da an nemi wuce makadi da rawa ba wajen gabatar da rahotannin da suka shafi harkokin rayuwar wasu shahararrun mutane masu zaman kansu, kuma ta haka alkalan suka sa kafa suka yi fatali da hukuncin da alkalan kotun koli ta Jamus suka zartas a game da cewar wadannan shahararrun mutane na daga cikin rukunin mutanen da talakawa ke koyi da su saboda tasirinsu a tarihi kuma a sakamakon haka ba laifi a gabatar da hotunansu ba tare da neman izini daga garesu ba. Amma fa a hakikanin gaskiya irin wannan damar ce a zamanin baya ta taimaka kafofin yada labarai na Jamus suka samu kafar fallasa tabargaza iri-iri da tona asirin ire-iren mutanen nan dake kiran tsuke bakin aljifu ga talakawa amma a daya bangaren suke facaka a rayuwarsu ta yau da kullum. Babban misali a nan shi ne tabargazar baya-bayan nan da aka fallasa dangane da tsofon gwamnan babban bankin Jamus, wanda ya amince bankin nan na Dresdner Bank ya dauki nauyin zamansa tare da iyalinsa a wani kasaitaccen otel a birnin Berlin, alhali kuwa doka ta haramta masa karbar duk wata kyauta ta alfarma. Ko kuma matar tsofon gwamnan jihar Sachsen, wacce ta dage akan neman rangwame akan wasu kayayyakin alatu da ta saya a wani kanti tana mai jefa ma’aikatan kantin cikin hali na kaka-nika-yi.

Irin wannan bincike domin tsage wa jama’a gaskiya yana da muhimmanci kuma za a ci gaba da yinsa, a sakamakon haka ne gwamnati a fadar mulki ta Berlin ba ta ga wani muhimmin dalili na daukaka kara akan hukuncin alkalan na kotun Turai dake birnin Strassburg ba, kamar yadda aka ji daga bakin ministar shari’a Brigitte Zypries. Bugu da kari kuma tilas ne a karya alkadarin ire-iren ‚yan jaridar nan ta kan wuce gona da iri wajen shisshigi a harkokin rayuwar mutane masu zaman kansu ba gaira ba dalili. To sai dai kuma duk wani mataki na kayyade ‚yancin ‚yan jarida, kamar yadda yake kunshe a hukuncin na kotun Turai, abu ne da zai gurbata yanayin ayyukan ‚yan jarida a nahiyar.