1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na daɗa yin tsamari a Kirgistan

June 15, 2010

Al'amura sai ƙara dagulewa suke yi dangane da rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a ƙasar Kirgistan dake can ƙuryar tsakiyar Asiya

https://p.dw.com/p/Nrai
Shugaba Bakiyev na Kirgistan mai murabusHoto: DW/Kesner

Yau tsawon kwana da kwanaki ke nan da tashe-tashen hankula suka zama ruwan dare a Kirgistan. Alƙaluman da aka bayar a hukumance sun nuna cewar mutane 170 suka yi asarar rayukansu, a yayinda ita kuma ƙungiyar UNICEF ta ce aƙalla mutane dubu ɗari ne ke kan gudun hijira a halin yanzu haka. Matsalar ƙabilanci dai ita ce ummal'aba'isin ƙazancewar tashe-tashen hankulan na baya-bayan nan. Amma a ina take ƙasa tana dabo ne dangane da wannan rikici na ƙabilanci.

Da farkon fari dai an fuskanci wata 'yar ƙwaya-ƙwaryar sararawar al'amura, kafin a sake faɗawa cikin mummunan tashintashina, watanni biyu kacal, bayan kifar da shugaba Kurmanbek Bakiyev da aka yi a tsofuwar janhuriyar ta Tarayyar Soviet dake tsakiyar Asiya. Tun abin da ya kama daga ranar alhamis ta makon jiya aka fara fuskantar tashe-tashen hankula a kewayen Osch, wanda shi ne birni na biyu mafi girma dake kurkusa da iyaka tsakanin Kirgistan da Uzbekistan. Wannan dai rikici yana da nasaba da tsofuwar gabar dake akwai tsakanin 'yan ƙabilar Kirgis da 'yan Uzbeki. Andrea Schmitz, ƙwaarriyar masaniya akan al'amuran yankin tsakiyar Asiya a cibiyar nazarin kimiyya da siyasa dake birnin Berlin tayi bayani akan haka tana mai cewar:

Unruhen in Kirgistan
'Yan sandan kwantar da tarzoma a KirgistanHoto: picture alliance / dpa

Ta ce:"Ainihin dalilin ƙazancewar tashe-tashen hankulan shi ne ƙyamar da 'yan Kirgis ke wa 'yan Uzbeki. Bisa ga ra'ayin 'yan Kirgis, 'yan Uzbeki dake yankin Osch na ƙwararsu a al'amuran rayuwa ta yau da kullum. A haƙiƙa dai ko da yake yawan 'yan Uzbeki bai wuce kashi 15 cikin ɗari na illahirin al'umar Kirgistan ba, amma a kudancin ƙasar yawansu ya zo daidai-wa-daida. Kuma a sakamakon ƙaurar da 'yan Kirgis suka riƙa yi zuwa yankin bayan rushewar daular tarayyar Soviet an samu ƙarancin kayan aiwatarwa, lamarin da ya sanya suke ganin wai ana ƙwararsu a al'amuran rayuwa a yankin."

Tun dai a zamanin baya yankin kewayen birnin Osch da ƙwazazzabon Fergana a kudancin Kirgistan ke zaman wani yanki na zaman ɗarɗar tsakanin ƙabilun guda biyu da ba su ga maciji da juna. Wannan ƙwazazzabon, wanda ya rabu zuwa ɓangarori uku tsakanin Kirgistan da Uzbekistan da Tajkistan 'yan ƙabilar Uzbeki ne suka fi rinjaye a wannan yanki. Yawa-yawancin mazauna yankin manoma ne masu ƙaƙarfan tushe na musulunci. Amma shi ma kansa kansa rikicin yana da ƙaƙƙarfan tushe mai daɗaɗɗ€n tarihi, kamar yadda Andrea Schmitz ta nunar.

Flüchtlingslager Kirgistan Kirgisistan Kirgisien
'yan gudun hijirar Kirgistan a iyaka da ƙasar UzbekistanHoto: AP

Ta ce:"Yankin ƙwazazzabon Fergana ya ƙunshi ƙabilu daban-daban tun fil-azal. Bayan shata iyakokin da tarayyar Soviet tayi a cikin shekarun 1920 da 1930 ne aka fara fuskantar matsala. A fafutukarta ta raba kawunan mutane don samun angizo, tarayyar Soviet tayi fatali da tsare-tsarinsu na zamantakewa, inda a yanzu haka zaka tarar da gungu-gungu na ƙabilun dake zaune ƙarƙashin ƙawanyar wasu ƙabilun dabam, kuma wannan shi ne ainihin matsalar dake akwai."

Wannan na ɗaya daga cikin musabbabin tashintashinar da aka fuskanta tsakanin Uzbekistan da Kirgistan a shekara ta 1990, inda aka halaka mutane kimanin 300 a ƙarkashin abin da aka kira kisan kiyashin Osch, kafin sojan tarayyar Soviet su shiga tsakani don raba faɗa. A kuma halin da ake ciki yanzu babu wata alama ta shawo kan rikicin na Kirgistan kamar yadda Andrea Schmitz ta nunar. Duka-duka abin da za a iya yi shi ne a lafar da ƙurarsa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Muhammed Nasiru Awal