1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na dada kazanta a Sri Lanka

Zainab A MohammedAugust 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5u

Jamian lura da yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin Sri Lanka sun ranta ana kare,sakamakon dauki ba dadi dake cigaba da gudana tsakanin mayakan kungiyar Tamil Tigers da jamian tsaro na gwamnati.Rahotannin daga kasar na nuni dacewa tawagar mai jamiai guda 6,ta fice daga sansaninta dake garin Trimcomalee ,wanda dake yankin gabashin Sri lanka,inda kuma ke cigaba da fuskantar arangama tsakanin dakarun gwamnati da mayakan adawa.Kakakin ayarin jamian lura da tsagaita wutan Thorfinnur Omarsson,yace sun fice daga wannan yanki ne saboda yadda fada ke dada kazanta tsakanin bangarorin biyu.Hukumar da aka nada domin lura da shirin tsagaita wuta da aka cimma a watan febrairun 2002,mai wakilai 54 akarkashin jagorancin Sweden dai,na rubuce kadai amma baa zahiri ba,.A yanzu haka dai akwai barazanar yiwuwar fadawar wannan tsibiri yakin basasa.Bangarorin biyu dake fada na cigaba da zargin juna,a wadannan rigingimu daya kashe mutane sama da 1,400 a hukumance,ayayinda wasu dubu 135 suka rasa matsugunnensu,daga watan Disamba kawo yanzu.