1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin Isra´ila da Palestinu

July 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bur4

Praministan Isra´ila Ehud Oplmert, yayi wasti da zargin da ƙungiyar gamayar Turai ta yi wa gwamnatin sa, a game da hare haren da ta ke kaiwa Palestinu, domin belin sojan ta ɗaya, da yan Hamas su ka yi garkuwa da shi.

Ranar juma´a da ta wuce ne, Ƙungiyar Gamayya Turai, ta yi Allah wadai, ga hare haren na Isra´ila, ta kuma gayyaci gwamnatin Hamas, da ta yi, iya ƙoƙarin ta, domin belin sojan na Isra´ila, wanda yau kwanaki 15, da ya ke tsare, a hanuwan yan Hamas.

A yayin da ya ke maida martani ga kiran EU Ehud Olmert ya bayana cewa.

A nasa ɓangare shugaban hukumar Hamas, Khaled Michael ,wanda a halin yanzu, ke gudun hijira a ƙasar Syria, ya tabbatar da cewa, ba za a samu bakin zaren warware wannan rikici ba , muddun Isra´ila ba ta amince ba, ta hurhura dubunan pirsinonin Palestinawa, da ta ke tsare da su, da wannan soja.

Khaled Mechhael ya ce, a halin da ake ciki, akwai pirsinoni dubu 10, Palestinawa, da su ka haɗa da ƙananan yara 400, da kuma mata 120, da Isra´ila ke tsare da su.