1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin Lebanon da Isra' ila

August 3, 2010

Wasu sojojin Isra'ila da na Lebanon sun rigamu gidan gaskiya a lokacin da suka bai wa hamata iska akan iyakar ƙasashen biyu.

https://p.dw.com/p/Ob2X
Hoto: AP

Aƙalla dakarun ƙasar Lebanon uku da kuma wani ɗan jarida ɗaya sun rigamu gidan gaskiya, yayin da wasu biyar suka ji rauni a lokacin da sojojin Isra' ila suka buɗe musu wuta a kan iyakar da ta raba ƙasashen biyu.  Bama-bamai biyu jirgin Isra' ila mai saukar ungulu ya harba akan motocin sulke Lebanon, tare da haddasa ƙonewar motocin da kuma salwantar rayukan sojoji da dama.

Isra' ila ta danganta harin, da martani da kashe mata wani injiniya da dakarun Lebanon suka yi. Rahotannin da suke zuwa mana daga birnin Beyrouth sun nunar da cewa fito na fiton yayi sanadiyar salwantar da rayukan sojojin Isra' Ila uku ciki har da wani hapsan soja.

 Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kudancin ƙasar ta Lebanon ta yi kira ga ɓangarorin biyu da suka kai hankali nesa, tare da tsakaita bude wuta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu