1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin Russia da Georgia

August 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuEM

Shugaban ƙasar Georgia Mikheil Saakachvili, ya zargi ƙasar Russia da kunna hasumi a Georgia.

HukumominTbilissi, sun tuhumi Russia ta harba wasu bama-bamai a Georgia da nufin tsokanar faɗa, kamar yadda ministan cikin gida Wano Merabischwili ya yi bayyana.

Shugaban ƙasar Georgia, ya bukaci Russia ta bada hujjoji a hukunce, a game da munufofin wannan hari.

Kazalika, ya yi kira ga ƙasashen ƙungiyar taraya turai, su hito fili ,su yi Allah wadai da wannan al´amari.

To saidai ba da wata-wata ba fadar mulkin Kremblin da ke birnin Mosko ta mussanta wannan zargi.

Mu´amila ta fara gurɓacewa tsakanin Russia da Georgia tun shekara ta 2003, a sakamakon hawan shugaba Mikheil Saakaschvili a kan karagar mulki, mutumen da Russia ke ɗauka a matasayin ɗan amshin shatan ƙasashen turai.