1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya da Armeniya sun ƙuduri sasantawa

April 24, 2009

An kama hanyar sulhu tsakanin Turkiya da Armeniya

https://p.dw.com/p/Hd8l
Ma´amila tsakanin Turkiya da ArmeniyaHoto: AP

Bayan shekaru kussan ɗari na gaba da juna, a yanzu ƙasashenTurkiya da Armeniya sun amince su zauna tebrin shawara da zumar cimma zaman lafiya.

Amurika da na Ƙungiyar Tarayya Turai sun taka muhimmiyar rawa wajen sasanta ƙasashen biyu.

Rikici tsakanin Turkiya da Armeniya ya samo asuli tun shekara ta 1915 a sakamakon kissan kiyasun da Armeniyawa ke zargin Turkawan Daular Otoman da aikatawa kansu.

Har yanzu ƙasar Turkiyya taƙi amincewa ta danganta tashe tashen hankulan a matsayin kissan kiyasu, domin akwai turkawa masu yawa da suka rasa rayuka a cikinsa.

wannan dangantaka ta kara tsami a shekara ta 1993, inda Turkiyya ta yanke shawara rufe iyakokinta ta Armeniya a wani mataki na nuna alhinini ga musulmin Azerbaijan.

Albarkacin cikwan shekaru 94 da ɓarkewar rikicin , ministan harakokin wajen Turkiyya, Ergemen Bagis ya sanar cewa, sun cimma yarjejeniya hawa tebrin shawara da Armeniya bisa jagorancin ƙasar Switzerland, ya kuma bayyana dalilin da ya sa ɗaukar wannan mataki:

Muna buƙatar ƙarfafa ma´mila da inganta maƙwabtaka ta hanyoyin cinikayya da cuɗe ni in cuɗe ka, cikin zaman lafiya.

A taƙaice dai, na hango cewar akwai cikkakar dama ta girka zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu.

Rikicin tsakanin Turkiya da Armeniya, bnatu dake ɗaukar hankali a fagen diplomatiya na duniya. A farkon makon da muke ciki ma,hukumomin Ankara sun buƙaci jikadan Turkiyya dake ƙasar Kanada ya dawo gida, bayan da Firaministan Kanada, ya bayyana wasu kalamomi masu ɗorawa Turkiyya alhakin aikata kissan kiyasun ga Armeniyawa.

A lokacin yaƙin zaɓe shugaban Amurika mai ci yanzu, ya hurta cewar da zaran ya samu nasara lashe zaɓe shima, zai amince da cewar Turkiya ta aikata leffin kisan kiyasu, to saidai akwai alamun Obama ya cenza tunani,ta la´kari da sabuwar dangataka tsakanin Amurika da Turkiya, kamar yadda Yasmin Congar wani Edita a jaridar Taraf dake Turkiyya ya nunar:

Fadar mulkin Washington na bukatar Turkiya ta buɗe iyakokinta da Armeniya ta na buƙatar Ankara da Yerevan sun daidai ma´amilarsu.

Saboda haka ne a ganina, Obama ba zai yarda, ya ambata kalmar kissan kiyasu ba.

A lokacin da ya kai ziyara a Turkiyya, shugaban ƙasar Amurika ya bayyana buƙatar ganin ƙasashen sun sasanta da juna.

Saboda haka nema,saɓanin sauran shugabanin Amurika da suka gabata, Barack Obama bai gabatar da jawabi ba, albarkacin zagayawar shekara ta kissan kiyasun, duk kuwa da matsin lambar da yake fuskanta.

Wannan saban yunƙurin ƙila zai cimma nasara ɗage takunkumin da Turkiya ta ƙargamawa Armeniya tun shekaru 16 da suka wuce, bayan da ta zargi hukumomin wannan ƙasa da mamaye kashi 20 cikin ɗari na Azerbaijan a sakamakon yaƙin basasar da ya ɓarke tsakanin Armeniyawa da Azarbaijawa.

Mawallafi: Jones/ Yahouza S. Madobi

Edita: Hauwa