Rikici ya ɓarke a zirin Gaza
June 14, 2007Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya kiri taron ƙoli, na hukumar zartaswa ta ƙungiyar fatah,da kuma PLO, domin tantana rikicin da ya turnuƙe, tsakanin Hamas da Fatah a zirin Gaza.
A tsukin sati 2 da su ka wuce, a ƙalla mutane 80 su ka rasa rayuka a cikin wannan rikici.
A yau alhamis, ƙarin wasu mutane 14, dukkan su na ɓangaren Fatah, su ka kwanta dama,a sanadiyar wannan tashe-tashen hankulla.
A halin da ake ciki, dakarun Hamas, sun bayyana kwace cibiyoyin tsaro na shugaban hukumar Palestinawa dake Gaza.
A yayin da ta ke huruci, a game da wannan abun al´ajabi, wakiliyar Palestinu a ƙungiyar tarayya Turai, Leila Shahid,ta ce nan gaba a yau , Mahamud Abbas, zai rushe gwamnatin haɗin kai da a aka girka tsakanin Fatah da Hamas.
A nasu ɓangare, ministocin harakokin waje na ƙasashen ƙungiyar musulmi ta dunia, OIC,sun bayyana adawa, ga matakin da Majalisar Ɗinkin Dunia ke shirin ɗauka, na tura dakarun shiga tsakani, a zirin Gaza.