1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya ɓarke tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati a DRC

August 7, 2006
https://p.dw.com/p/BunX

A yayin da al´ummomin Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ke cikin jiran sakamakon zaɓen yan majalisun dokoki da na shugaban ƙasa,wani saban yaƙi ya ɓarke a gabacin ƙasar, tsakanin dakarun gwamnati da na yan tawaye.

Dubun dubunan jama´a, na ci gaba da tserewa, daga wannan yanki da ke fama da ɓarin wuta.

Rahotani sun ce mutane 2, sun rasa rayuka, sannan 17 sun ji raunaka daga ɓangaren dakarun gwamnati.

Wannan saban yaƙi, ya ƙara saka al´ummomin ƙasar cikin zullumi.

Kazalika, jami´an bada agaji, na ƙasa da ƙasa, sun nuna damuwa,a kan yiwar ci gaba,da darkakawar yan tawayen, zuwa yankin Goma.

Dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia, sun fara sintiri, a birnin Goma, domin yi masa garkuwa da hare-haren yan tawaye.

Shugaban rundunar tawayen Laurent Nkunda,na fafatakar ƙwatar yancin yan ƙabilar tsutie, daga hukumomin Jamhuriya Demokradiyar Kongo.

Ƙungiyar gamayya turai da ƙungiyoyin sasanta rikicin ƙasar, sun yi kira ga ɓangarorin 2 su tsagaita wuta.

Kirere Mathias wani jami´in kiwan lahia da ke aiki a gabancin Kongo yayi huruci kamar haka.

A cikin wanan mawuyacin hali, abunda ke cikin zukatan mutanen Kongo, shine kwaɗayin samar da makoma kaukyawa, nan da ɗan lokaci ƙalilan.

Don cimma wannan buri, cilas,Kongo ta saka kuɗaɗe masu yawa, ta fannin gina assibitoci, makarantu, hanyoyi samar da ayyukan yi ga jama´a.

Shekaru da dama, gwamnati ta yi watsi da wannan ayyuka na ci gaba.