1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya barke a kasar Kongo Brazzaville

Zainab Mohammed AbubakarApril 4, 2016

Tun da sanyin safiyar yau ne fada da musayar wuta tsakanin wasu da ba'a tantance ko su wane ne ba da jami'an 'yan sanda a yankin kudancin birnin Brazzaville

https://p.dw.com/p/1IP8F
Kongo Brazzaville Rauch aus Verwaltungsgebäude
Hoto: Reuters/R. Bouka

Wadanda suka ganewa idanunsu sun shaidar da cewar, tun da misalin karfe biyu na dare ne aka fara jin karar harbe harben bindigogi a yankunan Makélékélé.da Mayana, wanda ya dauki tsawon sao'i hudu yana gudana babu kakkautawa. Kazalika an ji karar fashewar wasu abubuwa masu nasaba da nakiya.Barin wuta ba sabon abu ba ne a yankin kogin Kongo da ke arewacin birnin Kinshasa, fadar gwamnatin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo da ke makwabtaka.Shaidun sun bayyana cewar, rikicin ya ritsa da babban ofishin 'yan sanda da ke gunduwar Makélékélé.yankin da 'yan adawan Kongo ke da karfi.

Wakilin kamfanin dillancin labaru na Faransa na AFP ya shaidar da ganin mazauna yankin na tserewa daga gidajensu cikin yanayi na dimauta, domin neman mafaka a tsakiyar garin.

Wannan rikicin na zuwa ne a daidai lokacin da kotun tsarin mulkin Kasar ta Kongo ke nazarin halarcin sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana ranar 20 ga watan Maris, wanda shugaba mai ci Denis Sassou Nguesso ya lashe, sakamakon da manyan 'yan takara biyar suka yi watsi da shi bisa zargin tabka magudi.