1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RIKICI YAKI CI YAKI CINYEWA A GARIN NAJAF.

Maryam L.Dalhatu.August 12, 2004
https://p.dw.com/p/BvhK

A can kasar iraqi dai abin sai fatan Allah ya kara sauki domin kuwa wannan rikici na garin najaf tsakanin dakarun sojin amurka da kuma shiawa,kullum sai dada kazanta yake yi.

Kamar dai yadda rahotanni suka bayyana a safiyar yau sojin amurka sun fara amfani da jirage masu saukar ungulu da kuma manyan tankunan yaki wajen yakar shiawan.

Har ya zuwa yanzu dai amurkawan na nan sun yi garkuwa da babban masallacin shiawan,yayin da wasu kuma su kayi garkuwa da makabartar da aka binna ayyadina Ali.

Amurkawan basu da damar shiga cikin wannan masallaci,sai dai sojin iraqi da ke ta duruwa ciki don samun galabar wadannan shiawa da suka fake a cikin masallacin.

Su dai shiawan suna nan kann bakar su kamar yadda shugaban nasu Muqtadr Sadr ya gargadesu dayi na kada su kuskura su ajiye makamansu wato su mika wuya har sai inda karfin su ya kare ko kuma suka rasa rayukansu baki daya.

Mahukuntan kasar iraqi,da suka bawa sojin amurkan damar cigaba da farma shiawan a hannu guda sun gargade su da suyi a hankali da wannan masallaci da kuma makabartar.

Bisa dalilinsu na cewa yin illa ga wannan masallaci ko makabarta ka iya haifar da babban rikici a duk fadin kasar,kasancewar wadannan wurare masu tsarki ga yan darikar shiawa.

A yayin da ake wannan rikici a garin najaf,wata sabuwar ta balle a can garin kut,inda sojin amurka keta ruwan boma bomai don cimma shiawan dake wannan gari.

Wannan hari da amurkawan ke ta kaiwa,yayi sanadiyyar mutuwar mutane tamanin da takwas tare kuma da raunana wasu dari da tamanin.mafiya yawan wadannan mutane kuwa mata ne da yara a cewar wani jamiin maaikatar lafiya ta kasar.

A yammacin yau ne kuma aka gudanar da wani taron manema labaru a kasar na hadin gwiwa tsakanin ministan tsaro da kuma ministan cikin gidan kasar.

Ministocin biyu sun yi kira ne ga yan tawayen kasar da su yi hanzarin ajiye makamnansu don samar da kwanciyar hankali a kasar.a hannu daya kuma sun yi kira ga yan kasar dasu cigaba da bada goyon baya ga gwamnatin kasar don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Rahotanni daga kamfanin dillancin labaru na AP,sun bayyana cewa,hukumar zartarwa ta majalisar dinkin duniya ta bukaci majalisar data karawa jamianta lokacin aiki a iraqin zuwa wata shekara gudan.

Yin hakan a cewar hukumar zai taimaka wajen hada karfi da karfe tare da gwamnatin kasar iraqin don samar da matakan zaman lafiya a kasar tare da kawo karshen yan tawayen da suka addabi kasar baki daya.