1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ƙabilanci a Tchad

August 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuDG

A ƙalla mutane 15 su ka rasa rayuka,wasu da dama su ka ji raunuka, a wani rikicin ƙabilanci tsakanin yan ƙabilar Zaghawa ,da Tama a gabacin ƙasar Tchad.

Kakakin gwamnatin ƙasar Tchad, Hurmaji Musa Dungor, ya ce a halin yanzu kur ata klaffa, a sakamakon tsatsauran matakan da gwamnati ta ɗauka domin kawo ƙarshen wannan tashin hankali.

Rikici tsakanin ƙabilun 2, ya samo asuli daga tarihi, sai kuma a baya-bayanan ya ƙara ƙazamta, bayan da wani madugun yan tawayen ƙabilar Tama, ya bada goyan baya ga shugaban ƙasa Idris Deby Itno na ƙabilar Zaghawa.

Wannan rikici ya kara gurbata harakokin tsaro a yankin gabacin ƙasar Tchad, wanda ke fuskantar rikicin tawaye da kuma hare-hare, daga maƙwabiyar ta Sudan.

Gwamnatin ƙasar Tchad ta zargi Sudan da kunna mata rikicin tawaye ta hanyar anfani da yan gudun hijira Darfur da su ka sami matsuguni a gabacin ƙasar Tchad.