1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ƙabilanci ya yi ƙamari a ƙasar Kirgistan

June 14, 2010

Sama da mutane ɗari ne suka mutu a tashin hankalin da ake fama da shi a ƙasar Kirgistan

https://p.dw.com/p/Nq38
Hoto: AP

Kimanin mutane 117 suka rasa rayukansu a cikin rikicin ƙabilanci da ya auku a ƙasar Kirgistan, wanda a Garin Och aka samu mutane 92 da lamarin ya rutsa da su ,dakuma 21 a Djalalabad yayin da wasu 1500 suka samu raunika a rana ta ukku ta faɗan da ake yi tsakanin ƙabilun Kirze da Ouzbeks.Shedu daga yankin kudancin ƙasar inda lamarin ya yi ƙamari sun ce sun ga gawarwarki mutane zube barjat kan tituna, sanan gidaje da kantuna malakar yan ƙabilar Ouzbeks na ci da wuta

Ministan tsaro na ƙasar Pakistan ya sheda cewa yanzu haka an yi garkuwa da wasu yan ƙasar Pakistan 15 yayin da ɗaya ya rasa ransa a Garin Och a cikin faɗan.A halin da ake ciki ƙasar Rasha ta aike da sojoji lema aƙalla guda 150 a ƙasar ta Kirgistan domin kare wata cibiyar sojin ta da ke da sansani a ƙasar.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Mohammad Nasiru Awal