1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ƙasashen Sudan da Chadi

May 16, 2009

Har yanzu dai ana cigaba da zargin juna tsakanin Chadi da Sudan dake makwabtaka

https://p.dw.com/p/HroY
Omar al-Bashir,da Idris DebyHoto: AP

Gwamnatin Sudan ta zargi ƙasar Chadi da ƙaddamar da hare hare a yankunan dake ƙarƙashin ikonta, tare da bayyana cewar tilas ne a bi hanyoyin siyasa wajen warware rikicin dake tsakanin ƙasashen biyun dake makwabtaka da juna.

Kakakin sojojin Sudan, Uthman al-Aghbash, ya shaidawa manema labarai cewar, Chadi ta ƙaddamar da hare hare da jiragen samar yaƙi a yankunanta, amma ba tare da ya jikkata ko da mutum guda ba, yana mai karawa da cewar hanya ɗaya tilo ta shawo kan rigingimun dake ci gaba da wanzuwa tsakanin Chadi da Sudan, ita ce siyasa, ba wai ɗaukar matakan soji ba.

Sai dai kuma Kakakin gwambnatin Chadi, Mahamat Husseini, ya shaidawa manema labarai cewar, abin mamaki ne a ce mahukunta a birnin Khartoum na ƙasar Sudan su nuna game da matakin da Chadi ta dauka, yana mai cewar tsuntsun daya janyo ai shine ruwar zata daka.

Omar Hassan Ahmad al-Bashir Präsident Sudan
Omar Hassan al-BashirHoto: picture-alliance/ dpa

Ya ce duk wata taho mu gama tsakanin dakarun gwamnatin Chad da burbushin 'yan tawayen dake samun mafaka a Sudan, wadda ke makwabtaka da ita Chadin, yana mai cewar, wannan mummunan sakamakon hare-haren da ake kaddamarwa akan Chadi, waɗanda kuma masu tada ƙayar baya ke tsarawa, da bayar da horo game da samun kuɗaɗen gudanarwa daga mahukunta a birnin Khartoum na Sudan.

Tunda farko, Sudan ta zargi Chadi da laifin kaddamar da hari a yankunanta, kana ta ce rundunar sojinta zata mayar da martani kuma mafi muni, ko da yake ta ce Chadin ta kaddamar da hare-haren ne a wuraren da babu jama'a, kuma basu janyo wani lahani ba.

Wasu jiragen samar yakin Chadi sun kai hari a yankunan dake da tazarar kilomita sittin akan iyakar Sudan, inda rundunar sojin Sudan ta ce- a shirye take ta mayar da martani, amma tana jiran umarni ne kawai, kamar yadda Kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Sudan, Ali Sadiq ya fadi cikin wata sanarwa. Shi kuwa Kakakin gwamnatin Chadi Hussein cewa yayi idan Sudan bata shirya dakatar da tallafawa masu tada kayar baya ba, to kuwa Chadi zata ci gaba da lalata sansanonin bayar da haro ga masu tada zaune tsaye, da ma abinda ya kira shaidanu, yana mai cewar ba wai martanin da Sudan zata yi ne zai sa ta dakatar da kaddamar da hare hharen ba.

Tschad Präsident Idriss Deby
Idriss Deby ItnoHoto: AP

Chadi ta zargi Sudan da goyon bayan 'yan tawayen dake ƙoƙarin hamɓarar da gwamnatin Shugaba Idris Deby Itino na ƙasar, a yayin da mahukunta a birnin Khartoum kuwa ke zargin Chadi da tallafawa tsirarrun 'yan tawayen dake lardin Darfur.

A ranar huɗu ga watan mayu ne wasu 'yan tawaye suka kaddamar da hari akan birnin Njamena.

Manazarta na ganin zaman lafiya tsakanin Sudan da Chadi, waɗanda ke gaba da juna, nada muhimmancin gaske, wajen warware rikicin yankin Darfur, wanda aka yi tsawon shekaru shidda ana yi. A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, mutane dubu ɗari uku ne suka rasu sanadiyyar rikicin na Darfur, amma mahukunta a Sudan suka ce mutane dubu goma ne kachal.

Mawallafi: Umar Saleh Saleh

Edita: Zainab Mohammed