1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Amurka a Somalia

January 10, 2007

Cigaban wadannan hare hare da Amurkan ke kaiwa a kasar ta somalia na iya haifar mata da mai idanu,

https://p.dw.com/p/Btwh
Sabbin hare haren Amurka a Somalia
Sabbin hare haren Amurka a SomaliaHoto: AP
a kokarinta na yakar ayyukan tarzoma,sai dai baya ga kasar Britania,babu alamun goyon baya data samu dangane da wannan sabon yunkuri nata,inji Manasarta.

Kasashen gamayyar turai dai sune ke kann gaba na bayyana adawansu da wannan yunkuri na Amurka,dacewa matakin farko da somalian ke bukata a yanzu shine aiwatar da yiwuwan bayyana dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa da zasu taimaka wajen tabbatr da tsaro a wannan kasa.Kakakin maaikatar harkokin wajen faransa Jean-Baptiste Mattei,ya bayyana cewa wadannan hare hare da Amurka da Habasha ke kaiwa ,zasu dada dagula lamura ,tare da sake haifar da wasu sabbin rigingimu a wannan kasa da har yanzu bata zauna da gindinta ba.

Shi kuwa karamin minista a maaikatar harkokin wajen kasar NorwayRaymond Johansen,bayyana raayin kasarsa yayi dacewa Amurkan na iya yakar wadanda suka kaiwa ofisoshita hari a Tanzania da Kenya,amma zata iya yin hakan ne kadai ta hanyar cafkesu domin gurfanar dasu gaban hukuma.

Jamus wadda a yanzu ke rike da kujerar shugabancin kungiyar EU,ta bayyana cewa abu mafi mmuhimmanci das somalia ke bukata yanzu shine kai mata agajin kayayyakin masarufi ,tare da aiwatar da tattaunawar cikin gida ,wadanda sune tubalin janyewan dakarun Habasha daga cikin kasar bakai daya.

Kakakin maaikatar harkokin wajen jamaus Martin Jeager,yace abu mafi muhimmanci daya kamata a sanya fifiko akai a yanzu shine samaer da zaman lafiya a kasar asomalia.

To sai dai a nashi bangaren mataimakin shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar ta eu,Franco Frattini ya bada goyon bayansa ne wa Amurkan a yaki da kungiyar ta alqaeda.Ya fad ata kafofin yada labaru a Italia cewa,matsalar a halin yanzu ba Amurka bace,amma dole a yaki ayyukan tarzoma.Kazalika Prime minista Tony Blair na Britania,ya bayyana goyon bayansa wa wadannan hare haren da Amurka ke cigaba da kaiwa kudancin kasar ta Somalia,wanda kaweo yanzu ya haddasa mutuwan mutane akalla 19, ahukumance.

To sai dai ayayinda ake cikin wannan hali,mdd da komitin tsaro na Au na kokarin ganin cewa an samu shigar da dakarun kiyaye zaman lafiya dasu taimaka wajen daidaita lamura a wannan kasa,koda yake hakan zai dauki lokaci inji Ministar kula da harkokin waje na kasar Afrika ta kudu Nkosazawa Dlamini-Zuma.

Mdd takan dauki lokaci mai tsawo.Koda ta zartar da batun ayau ,zai kai kusan tsakiyar shekaran nan kafin a tabbatar dashi .Raayin mu anan shine, agaggauta yiwuwar tura dakarun tsaro wadanda ke shirya a yanzu.Kuma komitin sulhu da mdd zasu basu goyon baya da suke bukata.