1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Chadi da Sudan

April 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1s
Gwamnatin Chadi ta sake zargin makwaciyar ta Sudan da tallafawa tare da goyon bayan hare haren da ´yan tawaye suka kai akan wannan kasa dake tsakiyar nahiyar Afirka. A dai halin ciki shugaba Idris Deby ya rufe kan iyakar Chadi da Sudan, hakazalika ya katse huldar diplomasiya da gwamnatin birnin Khartoum. Akalla mutane 150 aka kashe a mummunan fadan da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da ´yan tawaye a Njadmena babban birnin Chadi a ranar alhamis da ta gabata. Shugaba Deby ya kuma yiwa gamaiyar kasa da kasa kashedi da ta nemo bakin zaren warware rikicin lardin Darfur dake iyaka da Chadi kafin watan yuni. Shugaban ya ce idan ba haka to dole a kwashe ´yan gudun hijirar Darfur su kimanin dubu 200 daga Chadi zuwa wani wuri dabam.