1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Dan-Kwali A Makarantun Jamus

May 18, 2004

Har yau ana ci gaba da kai ruwa rana dangane da maganar haramta dan-kwali ga malaman makaranta Musulmi lokacin da suke bakin aikinsu na koyarwa a makarantun gwamnati

https://p.dw.com/p/BvjT
Ana iya samun matan musulmi sanye da dan-kwali a duk fadin Jamus
Ana iya samun matan musulmi sanye da dan-kwali a duk fadin JamusHoto: AP

A lokacin da yake bayyana ra’ayin cibiyar ta Jamus akan hakkin dan-Adam, darektanta Heiner Bielefeldt nuni yayi da cewar, idan Musulmi masu zazzafan ra’ayin addini na kokarin mayar da maganar dan-kwalin ta zama wata manufa ta siyasa, wannan wata magana ce dabam, amma bai kamata gwamnati da mujami’u da sauran kungiyoyin dake da tasiri a tsakanin jama’a su nemi yayata maganar ba, abu mafi alheri shi ne su kakkabe ta daga manufofin siyasa. Cibiyar mai alhakin kula da matsaloli na cikin gida a karkashin laimar ma’aikatar shari’a da ta taimakon raya kasa, wacce aka kafa ta a shekara ta 2001, ta ce ko da yake dan-kwalin ka iya zama wata alama ta danniya ga mata, kamar yadda wasu ke ikirari, amma fa a daya bangaren, kazalika, yana iya zama wata shaida ga ‚yancin addini da Jamus ke tinkafo da shi. A saboda haka cibiyar ke da ra’ayin cewar wajibi ne a danka wa kotuna alhakin bitar lamarin a wawware a maimakon daukar wani mataki na bai daya domin haramta wa malaman makaranta Musulmi daura dan-kwali a ajujuwan koyarwa. Wannan maganar wajibi ne a tantance ta saboda ta shafi biyayya ne ga addini a bangare guda da kuma ‚yancin matan da lamarin ya shafa a karkashin manufar nan ta kamanta adalci tsakanin maza da mata, in ji darektan cibiyar Heiner Bielefeldt, wanda ya kara da cewar:

Bisa ga ra’ayinmu babban kuskure ne a yi saurin ba wa dan-kwalin ma’anar danniya ga mata. Abin ya danganci ita kanta matar da lamarin ya shafa ne da kuma matsayin da take dauke da shi. Wato dai a takaice ba zata yiwu a mayar da dan-kwali tamkar wani mizanin da za a auna alkiblar da wata malamar makaranta ta fuskanta kuma a saboda haka a haramta mata aiwatar da shi ba.

Wani babban rikicin dake akwai a game da wannan takaddamar shi ne neman da ake yi a banbanta ‚yancin addini ga malamai da ‚yan makaranta. Domin kuwa hujjar da ake bayarwa a game da haramta dan-kwalin shi ne na cewar mai koyarwar ka iya yin tasirin akidar addini a zukatan ‚yan makaranta. Wato ke nan za a take hakkin malamai domin girmama na 'yan makaranta. A saboda haka ya zama wajibi a danka wa kotuna alhakin lamarin saboda sune zasu iya tantance lamarin akan kowace malamar makarantar da lamarin ya shafa a wawware. Daga bisanin nan sai da tsofon shugaban kotun koli ta Jamus Ernst Mahrenholz ya fito fili yana mai gargadi a game da wani yunkuri na yi wa kowace mace dake sanye da dan kwali tambarin zazzafan akidar addini da fatali da daftarin tsarin mulkin kasa. Bai kamata a dora maganar akan dan kwali ba. Akwai makarantun allo, inda ake cusa wa yara irin wannan akida kuma anan ne za a iya tinkarar wannan ci gaba daga tushensa, amma ba a makarantun gwamnati dake karkashin kulawar mahukunta ba.