1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Darfur na ƙasar Sudan

May 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuLG

Tawagar haɗin gwiwa, da ta ƙunshi wakilan majalisar Ɗinkin Dunia, da na ƙungiyar taraya Afrika, na ci gaba da tantanawa da ɓangarori daban-daban masu yaƙar juna, a ƙasar Sudan ,da zumar samar da kwanciyar hankali mai ɗorerwa.

Jan Eliyasson, da Salim Ahmed Salim, da ke jagorantar wannan tawaga, sun yi taron manema labarai a birnin Khartum, inda su ka bayyana takaici, a game da hauhawar yaƙe-yaƙen ƙabilanci a yankin Darfur.

A ganawar da su ka yi da hukumomin Khartum, jami´an 2, sun, buƙaci dakarun gwamnati su daina kai hare-hare ga garuruwan Darfur.

A ɗaya hannun, sun yi kira ga yan tawayen yanki, su tsagaita wuta.

A mako mai zuwa, Majalisar Ɗinkin Dunia,ta ambata aika wata tawaga ta mussamman, a ƙasar Tchad, domin ganawa da hukumomin N`Dajmena, a kan rundunar haɗin gwiwa, da Majalisar zata tura, domin shiga tsakanin a wannan yanki mai fama da rigingimu.