Rikicin Darfur na shirin ɗaukar saban sallo
March 14, 2007Ƙasashe da ƙungiyoyin daban daban na dunia na ci gaba da matsa ƙaimi ga shugaban ƙasar Sudan Omar El Bashir, a game da rahoton Majalisar Ɗinkin Dunia mai bayyana wulaƙancin da hukumomin Khartum ke yi wa al´umomin yankin Darfur.
Amurika da Britania sun hiddo sanarwar yiwuwar ɗaukar mattakai tsatsaura, a kann Sudan muddun ta ƙi amincewa da karɓar dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfur.
Kazalika ƙasar France ta aika wasiƙa a ranar jiya, inda ta bayyana rashinamincewa da matakin fadar mulkin gwamnatin Sudan a game da wannan rikici.
Ya zuwa yanzu, Shugaba El Bashir ta bakin ministan shari´a Mohamed Ali Elmardi, yayi watsi da rahoton na Majalisar Dinkin Dunia, a game da tozarcin da ke wakana a Darfur.
A wani labarin kuma, ƙasar Rwanda ta yi barazanar janye dakarun ta daga wannan yanki, ta la´akari da karancin kayan aiki da rundunar shiga tsakani, ta tarayya Afrika ke fuskanta.
Gobe idan Alllah kai mu, komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, zai shirya zama na mussamman, a game da rikicin ƙasar Sudan.