1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Darfur

June 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuJV

Majalisar Ɗinkin Dunia na ci gaba da matsa kaimi ga ƙasar Sudan, a game da rikicin Darfur.

Komitin sulhu ya tabka mahaura mai zafi yamacin jiya a game da wannan batu, jikadan Amurika Zalmay Khalilzad, ya tabatar da cewa muddun hukumomin Sudan su ki bada haɗin kai cikin gaggawa, domin tura tawagar shiga tsakanin a yankin Darfur, to cilas Amurika ta gabatar da saban ƙuduri gaban Majalisar Ɗinkin Dunia.

A cikin ƙudurin Amurika zata buƙaci Majalisar, ta shata wani ziri, tsakanin yankin Darfur, da sauran ƙasar Sudan, wanda za a haramtawa jiragen samar Sudan shawagi a cikin sa.

Kamin ɗaukar wannan mataki, Amurika na jiran sakamakon tantanwar da wakilin komitin sulhu za su yi, da hukumomin Khartum, ranekun litinin ,da talata masu zuwa.

A nasa ɓangare shugaban kotin ƙasa da ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ya yi kira ga komitin sulhu, ya yi anfani da wannan ziyara, domin samun damar gurfanar da wani ministan ƙasar Sudan, da kuma shugaban ƙungiyar yan Djanjawid, da akewa zargin aikata kissan kiyasu.