1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Darfur

April 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuNU

Rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan, na ci gaba da fuskantar kon gaba kon baya.

A halin da ake ciki murna ta koma ciki, bayan amincewar da gwamnatin Sudan ta yi, a kan batun aika runduna sojojin shiga tsakani na Majalisar Ɗinkin Dunia su dubu 3, a Darfur,domin tabbatar da tsaro.

A yammcin jiya jami´an Majalisar Ɗinkin Dunia da na ƙungiyar taraya Afrika, su ka kammalla zaman taro a birnin New York na Amurika, inda su ka jaddada kira, ga hukumomin Khartum, su gaggauta bada izini ,ga sojojin na Majalisar Dinkin Dunia.

To saidai a wani abu mai kama da tunƙa da walwala Jaridar New York Times ta wallafa wani rahoton sirri, da ta samu daga jami´an diplomatia, inda Sudan ke buƙatar fakewa da dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia, domin ɓullo da wani saban sallo, na kai hare-hare, ga al´ummomin Darfur.

Sakamakon wani bincike, inji Jaridar, ya gano cewar, gwamnatin Sudan, ta yi anfani da launi, da kuma tutar Majalisar Ɗinkin Dunia, ga wani jirgin ta, wanda ta yi anfani da shi, domin kai hari a yankin Darfur.

Jaridar ta ce