1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin diplomasiya tsakanin Rasha da Georgia

September 30, 2006
https://p.dw.com/p/Buhz
Wata kotu a kasar Georgia ta tsohuwar TS ta tuhumi wasu jami´an soji Rasha su 4 da lafin yiwa kasar leken asiri sannan ta ba da umarnin da su ci-gaba da zama a gidan wakafi har nan da watanni biyu masu zuwa. A martanin da mayar Rasha ta janye jakadanta daga birnin Tiflis sannan ta fara kwashe jami´an ta na diplomasiya da iyalensu daga kasar ta Georgia. Kamun mutane su hudu ya ta kara dagula dangantaka tsakanin gwamnatin birnin Tiflis mai ra´ayin kasashen yamma da gwamnatin Mosko. A kuma halin da ake ciki ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung ya ce gwamnati a birnin Berlin ta damu game da mawuyacin halin da ake ciki. A lokacin da yake magana a gun taron ministocin tsaro na kasashen kungiyar NATO a Slovenia Jung ya yi kira ga sassan biyu da su warware wannan rikici cikin lumana.