1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Eritrea da Habasha - matsayin Majalisar Dinkin Duniya.

January 6, 2006

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya gabatar wa kwamitin sulhu wasu shirye-shirye game da yadda dakarun zaman lafiya da aka girke a kan iyakar kasashen Habasha da Eritrea, za su dinga gudanad da aikinsu.

https://p.dw.com/p/Bu2d
Taswirar Habsaha da Eritrea, da iyakar da ke tsakaninsu.
Taswirar Habsaha da Eritrea, da iyakar da ke tsakaninsu.Hoto: AP Graphics/DW

A halin yanzu dai, al’amura sai kara tabarbarewa suke yi a rikicin da kasashen Habasha da Eritrea ke yi a kan iyakarsu. Sabili da haka ne kuwa, Majalisar Dinkin Duniya ke gangami game da kasadar barkewar wani sabon yaki tsakanin kasashen biyu makwabtan juna. Babban sakataren Majlisar, Kofi Annan, ya bayyana cewa, rikicin zai iya janyo gagarumin cikas ga ayyukan da jami’an kare zaman lafiya da aka tura a yankin ke yi. Tun watanni da dama da suka wuce ne dai kasashen Habashan da Eritrea ke ta zargin juna da jan damara na shirye-shiryen yaki. Kazalika kuma, an yi ta lura da girke yawan dakarun bangarorin biyu a kan iyakarsu. A wani lokaci cikin watan Oktoban shekarar bara ma, sai da Eritrea ta umarci duk dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke girke a kasar, da su fice ma gaba daya.

Manazarta al’amuran yau da kullum a yankin, kamar Souleiman Baldo, na rukunin kasa da kasa mai kula da rikice-rikice, wato International Crisis Group, sun sha bayyana cewa wani mummunan yaki na barazanr barkewa tsakanin kasashen biyu da ke yankin kahon Afirka.

Kamar dai yadda Baldon ya bayyanar:-

„Al’amura sun cije ne, saboda babu mai kiyaye ka’idojin da aka amince a cikin yarjejeniyar zaman lafiyar nan da aka cim ma. Sanin kowa ne cewa, ita Habasha, ita ce ta ki yarda da layin iyakar da aka shata tsakaninta da makwabciyarta.“

Majalisar Dinkin Duniya ta tura dakarunta a yankin ne, don su sa ido wajen ganin cewa, kasashen biyu sun kiyaye ka’idojin yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cim ma a cikin shekara ta 2000, bayan wani mummunan yakin da suka gwabza da juna, inda kusan mutane dubu 80 suka rasa rayukansu. Yawan dakarun dai ya kai dubu 4 a halin yanzu, kuma mafi yawansu, sun fito ne daga Indiya, da Jordan da kuma Kenya.

Iyakar da ke tsakanin Habashan da Eritrea dai, ta yi tsawon kilomita dubu, kuma mafi yawan duk yankin da take bi, hamada ce inda babu mazauna da yawa a cikinta. A wani dan kauye mai suna Badme ne har ila yau kasashen biyu suka gaza amicewa da kudurin Majalisar Dinkin Duniya. Alkalan Majalisar dai sun yanke shawarar cewa, kauyen cikin harabar Eritrea yake, sabili da haka, kamata ya yi Habasha ta mayar mata da shi. Ita ko Habshan, sam ta nuna cewa ba ta san wannan zancen ba.

Kawo yanzu dai, gamayyar kasa da kasa da Kungiyar Tarayyar Afirka, sai kira ga bangarorin biyu kawai suka yi ta yi na su sasanta rikicin cikin ruwan sanyi. Ba su dau wani sashihin mataki ba. Wasu masu sukar lamiri kuwa na ganin cewa, kamata ya yi, duk wadanda suka taimaka wajen kulla yarjejeniya tsakanin kasashen biyu, bayan yakin da suka yi a shekara ta dubu 2, wato Majalisar Dinkin Duniya, da Amirka, da Kungiyar EU da kuma Kungiyar Tarayyar Afirka, su dau matakan bai daya na kara angaza musu don su amince da warware rikicin.