Rikicin Ethiopia da Erythrea
April 25, 2007Gwamnatin Adis Ababa, ta zargi Erythrea, da hannu a cikin harin da wasu mutane ɗauke da makamai, su ka abkwa wata tashar binciken man petur, da ke ƙasar Ethiopia ranar jiya talata.
A cikin wata sanarwa da ministan watsa kabarai na kasar Ethipia ta karanata ya ce ƙungiyar tawayen ONLF da ta daujki alhakinkai wannanhari a da alakarat kut da kut da fadar mulkinAsmara.
Babu shakka a cewar ministan Erythera ce, ta kitsa wannan hari da farko har ƙarshen sa, tare da haɗin gwiwar yan tawayen ONLF.
A saƙon yanar gizo da ta aika, wannan ƙungiyar tawaye da ke neman yancin yankin Ogaden na Ehtiopia, ta ce zata ci gaba da kai hare-hare, har sai ta cimma burin ta.
A nata ɓangare, Erythrea tunni ! ta maida martani, ga zargin na Ethiopia.
Kakakin gwamnatin ƙasar Ali Abdu,ya ce wannan zargi ba shi da tushe bare makama.