1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin gabashin Sudan

Zainab A MohammadJune 24, 2005

rikici ya barke a gabashin Sudan adai dai lokacin da ake kokarin warware na yammaci

https://p.dw.com/p/Bvb7
Hoto: AP

Wasu kungiyoyin yan adawa guda biyu a Sudan sun sanar dacewa gwamnatin Khartum ta kaddamar campaign din tayar da boma bomai a yankunan fararen hula a gabashin kasar ,akokarinta na dakatar da rikicin yan tawaye daya barke a wannan yankin.

Kungiyoyin wadanda suka afkawa sansanonin dakarun gwamnati a kudanci ranar lahadi tare da sanar da samun nasara tun sannan,sun zargi khartum da daukan matakai dasuka zo daidai da wanda tayi amfani dasu a lardin darfur dake yammacin wannan kasa.

Sun bayyana cewa harin boma boman dakarun gawamnatin ya fara ne a yankin Barka tun jiya alhamis,kuma yayi sakamakon jikkata fararen hula masu yawa ,wadanda yanzu haka ke jinya a asibitin garin Tokar mai tazarar km 120 ta kudanci.

Daya daga cikin manyan jamian kungiyar yan adawa ta Eastern Front,Salah Barqueen ya bayyanawa kamfanin dillancin labaru na reutres daga birnin asmara na Eritrea cewa ana cigaba da kaiwa fararen hulan yankin harin boma bomai,kuma mutane da dama sun samu raunuka,ko dayake babu cikakken adadi.Ya kara dacewa a yanzu haka an rufe babban asibitin garin Tokar saboda cunkoson majinyata,ayayinda aka kakkashe dabbobi da dama.

Mr Barqueen yace dakarun gwamnati na kai irin wadannan hare hare wa yankunan fararen hula ne domin bazasu iya fuskantar mayakan adawan kai tsaye ba.

To sai dai ya zuwa yanzu babu tabbaci dangane da wadannan rahotanni dangane da harin boma boman a wannan yanki dake tsakanin Sudan da Eritrea,sai dai a baya an zargi gwamnatin Khartum da kai harin boma bomai wa yankunan fararen hula a wuraren dake fama da rikici.

Shima babban jamiin kungiyar yan adawa ta Justice and Equality Movement watau JEM a takaice,wanda ke lardin Darfur Izzedine Baggi, yayi amana da wannan harin da wannan zargi da akewa dakarun gwamnati.

A jiya nedai kungiyar yan adawa ta Eastern front ta ce tankunan yaki da wasu masu dauke da makamai,mallakan gwamnatin Sudan sun bace a wannan yanki dake fama da rikici.

A dangane da hakane Mr Barqueen yace yana tsoro dangane da wannan aika aika da gwamnati keyi,domin bisa dukkan alamu tana iya yin kisan kiyashi wajen ganin cewa ta dakatar da hare haren yan adawa,tare da zargin gwamnan jihar Major general Hatim al-Wasilah al-sammani da hadin baki da gwamnati wajen daukan rayukan bayin Allah.

A watan febrairun wannan shekara nedai aka kirkiro kungiyar yan adawa ta eastern front,kungiyar dake wakiltar beja congress da free lions ,wadanda kuma a karo na farko suka kaddamar da harinsu wa dakarun gwamnati a kusa da garin Tokar ranar lahadi.

Kungiyoyin yan adawa na ganashi da yammacin Sudan din dai na zargin gwamnatin larabawa fararen fata dake Khartum dayiwa yankunansu wariya da danne musu hakkunansu a matsayin yan kasa,ayayinda gwamnati a nata bangare ke zargin gwamnatin Eritrea da samarwa yan adawa makamai.

Ayayinda ake kokarin kwantar da rikicin lardin Darfur dake yammaci,sai gashi kuma cikin wannan shekara rikicin gabashin Sudan din na neman sake mayar da hannun agogo baya.

Bugu da kari wannan ya sake kawo shakku dangane da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin khartum day an adawa na kudanci suka cimma a watan janairun wannan shekara,wanda ake ganin ya kawo karshen yakin basasa wanda ya dauki shekaru sama da 20 yana kudana a wannan kasa dake nahiyar Afrika.

A farkon wannan wata nedai tsohon madugun yan adawa dake kudanci Mr John Garang yakai ziyara birnin Asmara inda ya gana da magabatan Eritrea,ya kuma nuna tausayinsa wa kungiyar ta eastern front,kana ajiya Amurka tace tana ganawa da Mr Garang da wasu wakilai ta ofishin jakadancinta dake Sudan domin warware rikicin na gabashin Sudan.