1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Hamas da Fatah a yankin palasdinawa

Zainab A MohammadMay 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bu0I
Premiern Palasdinu Ismail Haniya
Premiern Palasdinu Ismail HaniyaHoto: AP

Prime ministan palasdinawa Ismail Haniya yayi kira da a kawo karshen zubar da jini sakamakon ,sakamakon fadan daya barke tsakanin yan hamas dana na fatah dake adawa ,fadan dayayi sanadiyyar rayukan mutane uku.

Mutane uku ne suka rigamu gidan gaskiya a yankin na palasdinawa sakamakon barkewar wannan fada a zirin gaza tsakanin dakarun dake marawa shugsaba Mahmud Abbas baya da kuma magoya bayan hamas mai mulkin yankin.

Wannan fada dai na mai kasancewa mai tsananin rikicin cikin gida a karon farko daya ritsa da bangarorin biyu,da hayewan Hamas karagar mulki.Fadan dai wanda ya auku a garin Khan Yunis dake kudancin gaza,ya samu tushe ne bisa ga sabanin raayi tsakanin shugaba Mahmud Abbas da Prime minister Ismail Haniya dangane da matsaloli na tsar9o a yankin,a wata ganawar da sukayi a karshen masko.

Abbas Da Haniya,wadanda jammiyyunsu sukayi nasara a zaben yan majalisa daya gudana a watan janairu,na cigaba fafatawa a dangane da madafan iko a gwamnatin yankin da hamas kewa jagoranci,musamman ma bangaren jamian tsaro,batu kuma daya fara razana alummomin yankin na palasdinawa.

A yayinda ake ta wannan,gobara ta barke a harabar majalisar dokokin dokokin Ramalla dake gabar yamma da kogin Jordan,sai dai babu wanada ya samu rauni.An dai danganta wannan gobara da lalacewar wutan lantarki.

Kakakin kungiyar hasmas Sami Abu Zuhri,ya bayyana cewa wannan rikici ya barke net un a daren jiya,lokacin da jamian tsaro daga kungiyar fatah suka sace jamian tsaron hamas guda uku.

Daga nan ne dakarun hamas din suka kewaye inda ake tsare day an uwansu uku,tare da cafke hudu daga cikin jamian tsaron na Fatah.

Tun a farkon fadan ne aka bindige jamiin hamas guda,kana na bangaren fata suma suka rasa rayukansu daga musayar harbin bindiga,akewaye na biyun wannan fada.Rahotanni dai na nuni dacewa akalla mutane 11 suka jikkata,ciki harda wata budurwa mai shekaru 16 da haihuwa.

A hannu guda kuma yan fatah din sun bayyana cewa fadan ya barke ne bayan da jamian yansandan da gwamnatin hamas ta nada,wanda shugaba Abbas yayi adawa dasu,sun cafke tare da tsare wani mai tsaron babban jamiin kungiyar fatahAsakamakon hakane yan hamas din sukayi ta harbin rokoki da gurneti,wa motocin jamian na fatah.Bayan saoi uku ana fafatawa ne aka samu tsagaita wuta,ayayinda shugabannin bangarorin biyu ke cigaba da kokarin sasantswa,tare da kare sake barkewar irin wannan rikici a yankin palasdinawan da a tuni ya fada halin ni yasu na karan ci kudade na gudanarwa.