1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Hamas da Israela a hannu daya kuma da Amurka

Ibrahim SaniFebruary 20, 2006

Kungiyyar Hamas ta masu kishin addinin Islama ta dukufa wajen nemarwa kanta makoma ta gari, bayan barazana da aka yi mata

https://p.dw.com/p/Bu1a
isma´il Haniyya
isma´il HaniyyaHoto: AP

A tun lokacin da aka rantsar da majalisar dokokin yankin Palasdinawa dake da rinjayen yan kungiyyar Hamas a cikin ta a makon daya gaba ta, gwamnatin Israela ta dukufa ka´in da na´in wajen ganin ta saka gwamnatin a cikin halin ni yasu.

Da farko dai mahukuntan na Israela sun dauki matakin dakatar da shigar kudaden haraji izuwa yankin, da kasar take tarawa a sakamakon shigi da ficin kayayyaki.

Bugu da kari kasar ta kuma dauki aniyar ganin babu wata kasa a duniya dake hulda da wannan gwamnati ta Hamas, har sai ta amince da ci gaban kasar a matsayin kasa.

Kafin dai daukar wannan mataki, Kasar Amurka, wacce ta kira kungiyyar ta Hamas da sunan yar ta´adda tuni tayi barazanar dakatar da irin tallafin raya kasa da take bawa yankin, matukar bata amince da kasancewar ci gaba da zaman kasar ta Israela ba.

Ya zuwa yanzu ma dai kasar ta Amurka ta dakatar da bawa yankin tallafi na Dala miliyan 234, kana a daya hannun tana neman dawowar Dala miliyan 50 da yankin bai riga ya kashe su ba.

Da alama dai tattaunawar dawowa da wadannan kudade zai kasance daya daga cikin batutuwan da shugaba Mahmud Abbas da kuma wakilin kasar ta Amurka a yankin gabas ta tsakiya, wato David Welch zasu tattauna a taron da zasu gudanar a ranar asabar mai zuwa.

Game kuwa da kokarin tursasawa gwamnatin ta Hamas yarda da kasancewar ci gaban kasar ta Israela ga abin da kakakin kungiyyar ta Hamas, wato Mushir Al Masri ke cewa...........

"Ba zamu taba yarda da Israela ba a matsayin abokiya, ballantana kuma da kasancewar ta a matsayin halastacciyar kasa"

Da alama dai kokarin da kasar Amurka da Israela keyi na mayar da gwamnatin ta Hamas saniyar ware ya fara cin tura, domin kuwa a farko farkon watan nan da muke ciki ne shugaba vladimir Putin na Russia ya mika goron gayyata ga kungiyyar ta Hamas don tattaunawa da ita a birnin Mosko.

Wannan dai bayani ya harzuka mahukuntan kasashen biyu, a inda ba tare da wani bata lokaci ba kasar ta Israela ta bukaci gwamnatin ta Russia data tura kana nan jami´an ta zuwa teburin tattaunawar da kungiyyar ta Hamas,a maimakon manya manyan jami´ai.

Har ilya yau kasar ta Israela da kuma Turkiyya sun fuskanci musayar miyau mai zafi, bayan da mahukuntan na Ankara suka yiwa jamian kungiyyar ta Hamas kyakkyawar tarba.

Bisa hakan dai kafafen yada labaru sun rawaito daya daga cikin jami´an diplomasiyya na Israela na fadin cewa hakan ka iya bata kyakkyawar dangantakar dake akwai a tsakanin su.