1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Hamas da Isra´ila

yahouza SadissouFebruary 3, 2006

Hamas ta yi tsayuwar gwamen jaki a kan akidar ta, ta haramta kasar Isra´ila

https://p.dw.com/p/Bu1r
Khaled Mechaal
Khaled MechaalHoto: AP

A na ci gaban da takon sako tsakanin kungiyar Hamas da ta lashe zaben yan majalisun dokokin Palestinu a makon da ya gabata, da kasashen dunia, mussaman Amerika da Turai, da ma wasu daga cikin kasashen larabawa da su ka bukaci kungiyar Hamas, ta kwance damara yaki, ta kuma amince da kasar Isreala.

Shugaban kasar Masar Hosni Mubarak, a wata hira da yayi yau da manema labarai, ya jaddada bukatar sa ta ganin kungiyar Hamas ta karbi kiran da kasashen dunia ke mata, na koma wa tebrin shawara da Israela, domin warwarware rikicin gabas ta tsakiya, cikin ruwan sanhi.

Idan basu cika wannan sharida ba, to ba maganar su girka gwamnati, inji, shugaban Mubarak.

A daya hannun, ya yi kira ga Israelawa, da su daina kururuwa da faduwar gaba, a sakamakon nasara da Hamas ta samu, a zaben yan majalisun dokokin.

Nan gaba a yau ne,shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, zai gana da tawagar kungiyar Hamas, inda zai bayyana bukatar Hamas ta daina haramta kasar Israela, ta kuma dauki mattakan zaman tantanawa da yahudawa.

A ranar laraba da ta wuce shugaban hukumar leken assiri na kasar Masar ya sanar cewa, Mahamud Abbas, ba zai ba yan Hamas damar girka gwamnati ba, muddun ba su amince ba, da Israela a matsayin kasa mai cikkaken yanci.

A nata gefe kasar Amerika ta bayyana dakatar da bada tallafi ga hukumar Palestinawa, a sakamakon wannna nasara da kungiyar Hamsar ta samu, a zaben ranar 25 ga watan da ya gabata.

Karamin jikadan kasar Amurika da ke birnin Kudus ya bayyana wa kampanin dullacin labaran Reuters cewar, gwamnati Amurika na kyauttata zaton yan Hamas sunyi amfani da wannan nasara da su ka samu, domin karfafa huldodi tsakanin su da kasar Iran, hakan kuwa, idan ta tabata, za ta kara dagulla harakoki a yankin ta gabas ta tsakiya.

Daya daga shugabanin kungiyar Hamas Khaleed Michaael ya kara maida martini ga kiranye kiranyen da dunia ke masu na aminicewa da kasar Israela.

Yace har Mahdi ya bayyana, Hamas ba za ta taba amincewa ba, da kasancewar Israela a matsayin kasa yanttata, muddun za ta ci gaba da kaka gida, a yankunan Palestinu.

A dalili da wannan tsatsauran mataki da Hamas ta dauka, Israela, ta yanke shawara dakatar da kudaden da ta ke zubawa hukumar Palestinawa a farkon ko wane wata, domin gudun, kar yan Hamas su yi anfani da wannan kuddade, a cikin ayyukan ta´adanci.

Wannan kudaden da yawan su ya tashi dalla million 40 zuwa 50, ko wane wata, na fitawa daga harajin awan kayan Palestinawa, da ke bi ta tashoshin jiragen ruwa, da na samar Israela.

Pramistan Palestinu mai barin gado, Ahmed Qorai, yace hukumar palestinawa, ta shiga tantanawa da wasu kasashen larabawa, domin samar da kudaden cika wannan gibi.

Kasar Amurika, ta alkawatra ciwo kan Israela ta ci gaba da zuba wannan kudade domin tallafawa shugaban Mahmud Abbas, wanda a hili ya bayana burin sa, na samar da masalaha cikin ruwan sanhi a rikicin yankin gabas ta tsakiya.