1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Iraki

Zainab A MohammadMay 5, 2005

Ana samun karuwan rikice rikice a Iraki

https://p.dw.com/p/Bvc8
Hoto: AP

Kasar Iraki na cigaba da fuskantar tashe tashen hankula daga sasas daban daban ,kama daga harin boma bomai zuwa kwanton bauna wa fararen hula da jamian tsaro.Wayewar gari yau alhamis mutane 24 suka rasa rayukansu daga fashewar boma bomai a kewayen birnin bagadaza.Wadannan hare hare na yau dai na masu kasancewa na baya bayan nan ,tun bayan nada sabuwar majalisar gudanarwa a wannan kasa.

Wani dan kunar bakin wake ya tayar da boma bomai dake jikinsa a cibiyar horar da sojoji a yammacin bagadaza,inda nan take mutane 13 suka rasa rayukansu,tare da raunana wasu 15.Yan kunar bakin wake a Irakin dai sun sha kai hare hare irin wadannan a cibiyoyin da ake shirin daukan jamian tsaro ko kuma horar da sabbi da aka dauka.

Bugu da kari wasu yan bindiga dadi sun yiwa ayarin motocin yansanda kwanton bauna ,inda suka bindige yansanda 10 tare da cinnawa motocinsu wuta.A hannu guda kuma bomb ya fashe a wata mota alokacinda ayarin motocin mataimakin ministan harkokin cikin gida ke wucewa,harin daya ritsa da ran daya daga cikin masu tsaronsa,tare da raunana wasu 6.

Duk da zaben daya gudana a wannan kasa,wanda kuma nadin sabuwar gwamnatin democradiyya ya biyo bayansa a makon daya gabata,yan yakin sunkuru na cigaba da kai hare hare babu kakkautawa musamman kan jamian tsaron Irakin da kuma baki na ketare musamman na Amurka da britania.

A jiya laraba,wani dan kunar bakin wake ya kasha kimanin mutane 60,a harin daya kaiwa ofishin jammiyar kurdawa,da cibiyar daukan yansanda dake garin Arbil a arewacin Bagadaza.Ayayinda tashin bomb a wata mota ya kasha sojojin Iraki 9 a kudancin Bagadaza.

A ranar talata ne aka rantsar da sabuwar gwamnatin democradiyya a Iraki,abunda jamian Amurka da Irakin sukayi fatan zai kawo zaman lafiya.Rikicin sassa daban daban na kasar kan madafan iko nedai ya janyo jinkiri wajen nadin sabuwar gwamnatin ,watanni uku bayan an gudanar da zabe,abunda kuma yan yakin sari ka noken suka dauki daman cin Karen su babu babbaka.

Duk dacewa an nada majalisar mulkin Irakin,har yanzu akwai gibi 5 dake jira a mayesu ,ciki kuwa harda maaikatun tsaron kasa da albarkatun mai,ayayinda a daya hannun jammiyyun siyasa ke cigaba da fafutukan neman mayesu.

Yanzu haka babu alamun cimma yunkurin samun zaman lafiya a wannan kasa,abunda zaa iya cewa ya jefa dakarun Amurka cikin hali na tsaka mai wuya,wadanda haryanzu ke jagorancin dakarun hadin gwiwan da suka mamaye Iraki,tun a watan maris din shekara ta 2003.

Yawancin kasashe da suka bada gudummowan sojoji dai sun janye su,cikin shekaru biyu da suka gabata.