1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RIKICIN IRAKI.

Zainab Mohammed.November 18, 2004
https://p.dw.com/p/BveW
Matatan Mai na garin Kirkut a Iraki.
Matatan Mai na garin Kirkut a Iraki.Hoto: AP

Acigaba da rikicin kasar Iraki,a yau ma wasu yan ta kifen kasar sun kai hari wa ofishin gwamnanan Mosul,dake zama mafi girma na uku.,inda sukayi nasaran kashe daya daga cikin masu tsaronsa tare da raunanan wasu guda 4.

Bugu da kari wasu yan Irakin guda 7 ne suka rasa rayukan su a yau alhamis,alokacin da wasu boma bomai da aka dasa guda 3 suka tashi a matatan mai dake Baiji da cibiyar hakan mai dake birnin Kirkut dake arewaci,ata bakin yansandan wannan kasa.

A harin rokoki da suka kaiwa ofishin gwamman rikon kwaryan na Mosul,yan yakin sari ka noken sun kone wata motar tankin mai dake tsaye kusa da Ofishin,ayayin da shi gwamna Duraiba Kashmoula ya tsira da ransa ba tarae da samun rauni ba.A watan Yulin daya gabata nedai aka kashe wannan ya maye gurbinsa a wannan mukamai dayake rike dashi a ahalin yanzu.

Yan yakin sunkurun sun kuma harba rokoki 6 wa sansanin dakarun sojin Amurka dake garin na Mosul,sai dai rahotanni na nuni dacewa babu wanda ya jikkata sakamakon wadannan hare hare.

Fada dai ya sake barkewa a garin na Mosul mai dauke da kimanin mutane million 2,tun bayan da dakarun Amurka suka afklawa Falluja,mai tazarar km 50 yammacin Bagadaza,tun kwanaki 10 da suka gabata.Tun bayan nana rikicin na Mosul ya barke ,inda yan yakin sari ka noken suka mamaye ofisoshin yansanda da dama a makaon daya gabata ,tare da mamaye wasu tutuna dake wannan birni.A dangane da hakane Dakarun Amurka suka kai hare hare da jiragen yaki,ayayin a halin yanzu aka girke Sojojin Irakin a wasu ofisoshin yansanda dake Mosul din.

To sai dai a garin Falluja da aka dauki kwanaki 10 ana fafatawa tsakanin bangarorin biyu,ayau alamura sun fara lafawa .Inda a halin yanzu wata tawagar yan Irakin a karkashin sa idon Dakarun Amurka ke tatattara abunda ya rage daga gawawwakin mutane dake baje a tituna wannan birni.Koda yake sojojin Amurkan sunce kalilan ne fararen hula daga cikin wadanda aka kashe daga wannan rikici,mazauna garin sun bayyana cewa mafi yawansu ne aka fi kashewa.Babu dai cikakaken adadin fararen hula da suka rasa rayukan nasu a Fallujan.Dakarun na Amurka dai sunyi ikirarain cewa sun kashe 1,000 daga cikin yan yakin sunkurun dubu 2 zuwa 3 a wannan fafatawa.

A fadar gwamnatin Iraki dake Bagadaza kuwa ,wani bomb da aka dasa a gefen hanya ya tarwatse,wanda ya haddasa mutuwan dan kasar Iraki guda ,ayayinda guda ya samu rauni.

Ayau ne kuma prime ministan Australia John howard ya fadawa majalisar dokokin kasar cewa an gano gawan jamiar agaji kuma yar kasar Britania data kasance a aIraki na tsawon shekaru 30,wadda kuma akayiwa kisan gilla Magret Hassan mai shekaru 59 da haihuwa,a garin Falluja,sai dai daga baya ya janye wannan furuci da yayi.Wani Jamiin ofishin Jakadancin Britania dake Iraki,ya fadawa kamfanin dillancin labaru na reutrs cewa babu tabbacin cewa wannan gawar na Magret Hassan ne,sai dai ana cigaba da bincike.

Tun a ranar 19 ga watan Oktoba nedai aka sace Magret Hassa da aka haifa a birnin Dublin,wadda kuma kafin gamuwa da ajalin nata jamia ce ta kungiyar bada agajin kasa da kasa ta Care International a Irakin.Sai dai har yanzu baa gano wadanda suka sace ta ba,balle inda aka kaita ,har ta gamu da ajalinta a hannun su.