1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Iran da Britania

March 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuOr

Sakatare General na mdd ya tattauna batun tsare yan kasar Britania guda 15,da ministan harkokin waje na kasar Iran Manouchehr Mottaki, abirnin Riyadh din kasar saudi arabia.Majiya daga tawagar jagoran mdd ya fadaw manema labaru cewa magabatan biyu sun tattauna matsalar sojin na Britania guda 15,tattaunawar data daukesu tsawon sama da saa guda.To sai dai babu karin bayani dangane da sakamakon wannan ganawa tsakanin Ban ki Moon da kuma ministan harkokin waje na Iran.Britania dai ta bayyana cewa jamian nata suna kogunan kasar Iraki ne lokacin da dakarun Iran suka cafkesu,ayayinda hukumomin Iran suka hakikance cewa sun cafke su a cikin harabar kasar ta Iran.Britaniyawan dai sun harzuka sakamakon nuna jamiansu nasu jiya ta kafofin yada labaran kasar ta Iran,musamman bayanan Faye Turney,wadda ta tabbatar dacewa sun shiga kasar ta Iran.