1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin iskar gas tsakanin Georgia da Rasha

January 22, 2006
https://p.dw.com/p/BvB5

Shugaban kasar Georgia Michail Saakashvili ya zargi Rasha da katse tura mata iskar gas. Shugaban ya ce Rasha na tafiyar da wani shirin yiwa tsarin samar da makamashi a Georgia zagon kasa. Fashewar wasu abubuwa biyu a kan bututun gas dake bangaren Rasha ya gurgunta aikin tura gas din zuwa Georgia da Armenia. Hukumomin Rasha na zargin ´yan tawaye da hannu a wannan aika-aika. Shugaba Saakashvili ya bayyana wannan lamarin da cewa wani yunkuri ne na matsawa kasar sa lamba inda ya ce yanzu kasar na fuskantar matsalar karancin makamashi kamar a Ukraine. A lokacin da ya ke mayar da martani ga furucin na shugaba Saakashvili wani kakakin kamfanin samar da gas na Rasha wato gasprom ya ce bai kamata a sanya wata siyasa a cikin halin da ake ciki. Kamfanin Gasprom ya ce zai fara tura iskar gas zuwa Georgia ta wani bututu dabam.