1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Israila da Lebanon

July 19, 2006

Alámura na kara tabarbarewa a Lebanon tun bayan barkewar fada tsakanin sojin Israila da Hizbullah

https://p.dw.com/p/Btz0
Wasu daga cikin gine-ginen da Israila da ragargaza a Lebanon
Wasu daga cikin gine-ginen da Israila da ragargaza a LebanonHoto: AP

A ƙalla mutane 55 ne suka rasa rayukan su yayin da jiragen saman Israila da jiragen ruwan yaƙi suka yi luguden wuta a kan birane da kauyuka a faɗin ƙasar Lebanon a ranar larabar nan, yayin da a waje guda kuma dubban jamaá suke ta ficewa domin gujewa faɗan wanda bangarorin biyu suka yi kashedi da cewa ba shi da iyaka.

Hare haren wanda ke zama mafi muni tun bayan barkewar faɗan kwanaki takwas da suka wuce, ya hallaka sojin Israila biyu da kuma yahudawa uku fararen hula wanɗanda suka haɗa da ƙananan yara biyu.

Daruruwan yan ƙasar Lebanon ɗin sun ƙauracewa gidajen su domin neman mafaka a wasu wurare yayin da dubban yan ƙasashe ƙetare yawacin su yan ƙasashen turai ake ta kwashe su ta jiragen ruwa daga Beirut zuwa tsibirin Cyprus.

Majalisar ɗinkin duniya ta yi kashedi da cewa jamaá sun shiga mawuyacin hali, inda ya zuwa wannan lokaci mutane fiye da 500,000 suka tagaira a sakamakon farmakin da Israila ke cigaba da yi wanda ya hallaka mutane 310 a Lebanon kawai.

Shugaban hukumar taimakon agajin gaggawa na Majalisar ɗinkin duniya Jan Egeland na da matuƙar ban takaici.Yace halin da ake ciki ya munana, kuma yana kan tabarbarewa, dubban jamaá sun tagaiyara suna guduwa zuwa Syria, wasu sun nufi kan tsaunuka a Lebanon yayin da wasu suka nemi mafaka wajen abokai da Aminai a wasu wurare. Akwai kuma dubban mutane waɗanda a yanzu haka suke tsugune a gine- ginen makarantu.

Yayin da gamaiyar ƙasa da ƙasa suka kasa cimma matsaya a game da kiran tsagaita wuta, a ɗaya bangaren kuma Israila, ta lashi takobin cigaba da matsanancin yaƙi da Hizbullah har sai abin da hali yayi. Majalisar zartarwar Israilan ta gudanar da taro inda ta zartar da ƙudirin cigaba da kai hari Lebanon da Gaza ba tare da wani lokaci na kawo karshen sa ba.

A nasa ɓangaren, shugaban Hizbullah Hassan Nasrallah, ya ci alwashin cigaba da kai hare haren rokoki zuwa Israila har tsawon watanni ba kawai yan kwanaki ko kuma makwanni ba.

Mukaddashin sakataren Majalisar dinkin duniya Mark Mallock Brown ya yi tsokaci a game da rikicin da cewa suna cikin damuwa a kulli yaumin, bisa yadda faɗan ke cigaba, fararen hula daga ɓangarorin biyu sun sami kan su a cikin wani hali mawuyaci, kuma bisa ga dukkan alamu babu wata aniya daga ɓangarorin biyu na dakatar da faɗan da suke yi, ballantana su daina kai hari a kan fararen hula. yace matakin warware matsalar shi ne kwamitin sulhu na Majalisar ɗinkin duniya, to amma har yanzu alámura sun faskara wajen ganin kwamitin ya cimma manufa ta bai daya a kan batun, balle ma ya zartar da wani ƙudiri ƙwaƙwara.

Shi ma jamiin harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Javier Solana wanda ya yi kira da babbar murya ga dukkan masu faɗa aji da za su sanya baki cikin gaggawa domin kawo ƙarshen faɗan.

Israilan ta ƙaddamar da farmakin soji a kan arewacin Lebanon ne bayan sace sojojin ta biyu da yan Hizbullah suka yi a makon da ya gabata, yayin da kuma ta kashe wasu sojojin takwas a ɗauki ba daɗi. Hakan kuwa ya zo bayan sace wani sojin Israilan da yan gwagwarmayar Palasɗinawa suka yi a Gaza wanda shima ya janyo makamancin wannan farmaki.

A ranar larabar nan kuma wasu sojin Israin biyu sun rasa rayukan su yayin da wasu guda tara suka jikata a ɗauki ba daɗin da suka yi da yan Hizbullah.

Majalisar ɗinkin duniya dai na wani shiri na tura sojojin kiyaye zaman lafiya na gamaiyar ƙasa da ƙasa domin dawo da zaman lafiya a ƙasar Lebanon, to amma shugaban Amurka Geor W Bush wanda ya baiyana cewa Israila na da cikakkiyar damar kare kan ta ya kafe cewa sai an jawa Hizbullah da Syria linzami kafin a sami zaman lafiya mai dorewa a yankin.