1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin israila da palasdinu

Zainab A MohammedJune 27, 2006
https://p.dw.com/p/Btzb
Tankunan yakin israela a kan iyakar gaza
Tankunan yakin israela a kan iyakar gazaHoto: AP

Israela na dada jibge dubban dakarun akan iyakar zirin Gaza,a dangane da kasancewa cikin shirin kota kwana,sakamakon sace jamiin soji guda,da sojin sakai na palasdinu sukayi.

A halin da ake ciki yanzu haka dai palasdinawan da suka sace wannan jamiin sojin Israela,sun lashi takobin cewa bazasu sake ba har sai yahudawan sun sako dukkan mata da yara kanana da suke tsare dasu a kurkunsu,batun da kuwa tuni prime ministan Izraela ehud Olmert yace bazata yiwu ba.

Jamiin izraela,mai shekaru 19 da haihuwa kuma haifaffan dan kasar Faransa,ya fada hannun sojin sakai na palasdinawan ne ,a somame da suka kai wajen matsugunin sojin izraelan dake kan iyakar gaza,hargitsin daya haddasa mutuwan dakarun izraela guda biyu da mayakan palasdinu guda biyu.

A dangane da wannan hali da ake ciki sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice tayi kira ga izraela data bawa matakan diplomasiyya dama wajen warware wannan sabon rikici,inda ta kara dacewa ana daukan matakai da suka dace wajen ganin cewa an sako Kofur Gilad Shalit.

Duk dacewa Izraela ta amince dabin hanyar diplomasiyya wajen ganin cewa an sako jamiin nata,tuni dai palasdinawa dake da gidajensu akan iyakar gazan suka tsere,domin gudun yadda dakarun izraelan zasu afka musu ,ayayinda sojojin sakai dake gudun kisan gilla suka shiga buya.

A rana ta uku da barkewar wannan rikici dai,ministan tsaron Izraela Amir Peretz yayi rangadin ayarin dakarun da aka jibge,wandanda ke tsare da dukkan kan iyakokin gazan,bisa gudun cewa palasdinawan na iya fitar da Mr shalit zuwa wata kasa.

Akan haka ne ministan tsaron ya fadawa manema labaru cewa,dole zaa hukunta wadanda keda alhakin sace jamiin sojin nasu.Premien Izraela Olmert,wanda ke fuskantar kalubalensa na farko,da hayewansa karagar mulki a watan maris,yayi gargadin cewa,babu wata tattaunawa da zaayi da wadanda suka saje sojan.

Harin na ranar lahadi da safiya,inda sojojin sakai daga kungiyar hamas da wasu kungiyoyin palasdindu,dauke da makamai suka kutsa yankin iszarela dake kan iyakar zirin gaza,na mai zama hari matsananci na farko a wannan yankin,tun bayan da dakarun izraelan suka janye daga zirin gaza a bara.

A yanzu haka dai ana takun saka tsakanin magabatan izraelan dana palasdinu,bisa ga matsin lamban tabbartar dacewa an sako kofur Shalit a raye,batu kuma dake zama mafi muni ,tun bayan da hamas ta kafa gwamnati a yankin a watan maris.

Izraelan dai a yanzu hakas ta jibge tankunan yaki a filayen gonaki dake kusa da garin kerem shalom dake kan iyakar zirin gaza da kasar ta izraela,inda bakin bindigoginsu ke kallon yankin palasdinawa,da yawan dakarun soji 5,000.

Yanzu haka dai gwamnatin yankin palasdinwan na cikin wani wadi na tsaka mai wuya a dangane da karancin kudade na gudanarwa.Akan hakane wani ministan yankin yayi gargadin cewa izaraela na iya kutsawa Gaza ta sace rabin jamian gwamnatin hamas,ba tare da wata matsala ba.