1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ivory Coast a Watan Maris.

May 4, 2004

Rahotan majalisar dunkin duniya kan rikicin Abidjam.

https://p.dw.com/p/Bvk3
Hukumar kare hakkin biladama ta MDD ta Soki jamian tsaro a Abidjam.-
Hukumar kare hakkin biladama ta MDD ta Soki jamian tsaro a Abidjam.-

Rahotan na majalisar dunkin duniya na nuni dacewa jamian tsaro a kasar ta Ivory coast,sun haddasa sarana rayukan mutane akalla 120 fararen hula ,a wani sumame da sukayi ,dangane da hana gudanar da gangami na yan adawa a watan Maris.Rahotan wanada kamfanin dillancin labaru na Reuters ta yayata,na bayyana yadda jamian tsaron kasar suka shirya gudanar da wannan aika aika tare kuma da wasu yan ta kife a birnin Abidjam,babban cibiyar cinikayya na wannan kasa,bisa ga umurni daga hukumomin wannan kasa.

A wannan yamutsin dai akalla mutane 120,suka rigamu gidan gaskiya,ayayinda wasu 274 suka samu raunuka,kana ya zuwa yanzu babu wanda yasan makomar mutane 20 da suka bata,tun daga wancan lokacin.To sai dai rahoton hukumar kare hakkin bilaadama na Majalisar dake binciken wannan lamari,sun tabbatar dacewa ba iyakan adadin da hukumomi suka bayyana bane.

Rahotan kazali na bayyana yamutsin daya gudana ranakku 25 da 26 na watan na maris da kasancewa mafi munin yanayi na kisan gilla wa fararen hula ,babu gaira babu dalili,wanda ke zama keta hakkin dan adam.Rahotan yace akasarin kisan da akayi a wannnan rana ba akan tituna bane kamar yadda aka sanar,amma cikin gidajen wadanda ke shirin gudanar da wannan zanga zanga,dama wasu bayin Allah da basu da masaniya dangane da wannan batu,saboda kawai sunayensu da kuma tushen alummar da suka fito.Bugu dakari wasu yan sanda biyu sun gamu da ajalinsu ta hanya mafi muni na zalunci alokacin wannan rikicin.

Rahotannin gwamnatin kasar dai yayi nuni dacewa mutane 37 kadai suka rasa rayukansu.Yan adawan kasar ta Cotedivoire wadanda suka janye ministocinsu daga gwamnatin rikon kwarya da Laurent Gbagbo kewa jagoranci sun bayyana adadin akalla mutane tsakanin 350-500,wadanda suka rasa rayukansu a wannan rikici na watan maris.

Kakakin rundunar Sojin kasar ya bayyana cewa har yanzu babu martani dangane da wannan rahoto da MDD ta gabatar kann wannan batu.Da farko dai wakilin Ivory Coast a majalisar Dunkin duniya,na shirin gudanar da taron manema labaru a birnin New york ayau,amma a halin da ake ciki an dage ya zuwa gobe laraba,koda yake babu wani bayani dangane da dagewan.

A watan satumban shekara ta 2002 nedai Ivory coast kasar data fi kowacce arzikin coco a duniya ta fada yakin basasa,sakamakon yunkurin juyin mulki dayaci tura,domin hambarar da gwamnatin shugaba Gbagbo.Dubban mutane suka rasa rayukansu,banda sama da milion da suke tsere daga gidajensu.A watan Yulin shekarar data gabata ne aka sanar da kawo karshen yakin a hukumance,amma ya zuwa yanzu kasar mai yaawan alumma million 16 na rarrabe ,wanda yayi sanadiyyar rikice rikicen kabilanci,tasakanin kudanci dake karkashin gwamnati da arewaci dake hannun yan tawaye.

Rahotan na MDD yayi nuni dacewa Jamian tsaron sunyi amfani da yamutsin na watan Maris wajen,kai hari wa yan kasashen Burkina Faso,Mali da Niger dake makwabtaka da kasar kuma keda dangantaka ta kut da kut da yan adawan dake arewacin,kann abunda suka kira yan adawa da gwamnati.