1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin jammiyyar Likud a Izraela

Zainab A MohammadNovember 8, 2005
https://p.dw.com/p/Bu4P
Hoto: AP

Rikicin cikin gida da jammiyar prime minister Ariel Sharon na Israela ke fuskanta ,na iya jawo gudanar da zabe cikin gaggawa a wannan kasa.

Bisa dukkan alamu rikicin daya barke tsakanin masu adawa na jamiiyyar Likud da prime minister Ariel Sharon ,zai tilasta batun gudanar da zabe da wuri ,wanda zai taallaka da kuriar shugabanci da jammiyar hadin gwiwa ta Labour dake yankin.

A jiya nedai bangaren priome minister Sharon ya sha kaye a majalisar dokoki dangane da nadin minostoci biyu,batu da Sharon yace zai haifar da matsaloli a jammiyarsa ta Likud .Benjamin Natanyahu nedai yake jagorantar bangaren dake adawa da Sharon,mutumin da baya boye fatarsa na kiran premiern daga jamiyar ta Likud,tare dam aye gurbinsa a matsayin prime ministan Izraela.

Da matsayar da ake fuskanta a jammiyar Labour a dangane da batun jagoranci,akwai alamun cewa zaa samu sabanin raayi wanda zai haifar da matsala gabannin kasafin kudi na shekara ta 2006,batu da gwamnatin Sharon din nada waadi harya zuwa 31 ga watan Maris ,na tilasta gabatar dashi gaban majalisar dokokin kasar.

Idan har gwamnati batayi nasaran samun rinjaye ba,wanda yanzu bata dashi,to babu shakka gwamnastin zata rushe,wanda kuma zai jagoranci a gudanar da zabe da wuri,a maimakon watan Nuwamban shekara mai zuwa .

Yan adawa na jammiyar Likud din dai sunyi barazanar yin adawa da kasafin kudin,idan har gwamnati batayi musu isasshen kasafi adangane da yankunan gabon yamma da kogin Jordan da aka mamaye ba,tare da kebe kudi wa kimanin yahudawa yan kama wuri zauna 8,000 da aka kwashe da zirin gaza.

To sai dai wani na hannun daman Sharon ya fadawa manema labaru cewa,yiyuwan zabe da wuri a izraelan zai dogara ne a dangane da sakamakonzaben shugabannin na jammiyar Labour.

Kuriar raayin jamaa da aka gudanar ayanzu haka dai na nuni dacewa an jammiyar Labour na yanzu kuma mataimakin prime minister Shimon Peres,bisa dukkan alamu zai doke abokin takararsa Amir peretz,watau babban sakatare na kungiyar Histadrut.

Idan hakan ya kasance to babu shakka Sharon zai cigaba da mulki,amma idan Amir Peretz ya samu nasara,babu kasasfin kudi kenan ,kuma hakan na nufin zaa rusa majalisar dokoki.

Rikicin na jammiyar ta Likud dai ya samo asali ne daga janye yadudawa yan kama wuri zauna da dakarun Izraela daga matsugunnensu dake zinin gaza,bayan mamaye na tsawon shekaru 38.

Ministan harkokin wajen izraela Silvan shalom yayi gargadin cewa fadan cikin gida da jammiyar Likud ke fama dashi ,na tabbatar da cewa jammiya bazata sake samun nasaran data samu a zaben watan janairun 2003 ba,wanda a wancan lokacin a karkashin jagorancin Sharon,ta samun lashe kashi 1 bisa 3 yawan kujeru 120 dake majalisar dokokin kasar.