1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kabilanci a Kwango ya lakume rayuka

Yusuf Bala Nayaya
February 28, 2018

A shekarar 2017 ma dai gwamman mutane ne suka mutu bayan fadan da a ka yi a kauyukan Bwalanda da Mutanda da Kikuku inda a ke yawan samun fadace-fadace.

https://p.dw.com/p/2tSLd
Kongo Kämpfe in in Goma
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Kay

Mutane 23 ne suka hallaka bayan da wani fadan kabilanci ya barke a gabashi na Jamhuriyar Demokradiyar Kwango kamar yadda jami'ai suka bayyana a wannan rana ta Laraba. Rikicin da ya barke a yankin Rutshuru da ke a lardin arewacin Kivu da yaki ya daidaita ya faru ne tsakanin al'ummar Hutu da Nande da Hundu a wani bangaren.

Mai taimaka wa gwamnan lardin na Kivu Francois Bakundakabo ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa daga bangarensu sun samu labarin mutuwar mutane 16 fararen hula da kuma bakwai masu tada kayar baya a bayanan da suka tattara a ranar Lahadi. A shekarar 2017 ma dai gwamman mutane ne suka mutu bayan fadan da aka yi a kauyukan Bwalanda da Mutanda da Kikuku inda a ke yawan samun fadace-fadace. 'Yan kabilar ta Nande da Hunde dai na kallon 'yan Hutu a matsayin 'yan tawaye baki masu alaka da 'yan kabilar Hutu na Ruwanda.