Rikicin kabilanci ya barke a Kwango
March 3, 2018Talla
Masu aiko da rahotannin sun ce fadan da aka gwabza tsakanin makiyya 'yan kabilar Lendu da manoma 'yan kabilar Hema ya rutsa da mata da kuma yara kanana. Fada tsakanin kabilun Lendu da Hema wanda ke zaman tsohuwar gaba a tsakaninsu tun daga shekara ta 1999 ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu sitin kawo yanzu.